Zabura 32
Ta Dawuda. Maskil* ne.
Mai farin ciki ne shi
wanda aka gafarta masa laifofinsa,
wanda aka shafe zunubansa.
Mai farin ciki ne mutumin
da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa
wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.
 
Sa’ad da na yi shiru,
ƙasusuwana sun yi ta mutuwa
cikin nishina dukan yini.
Gama dare da rana
hannunka yana da nauyi a kaina;
an shanye ƙarfina ƙaf
sai ka ce a zafin bazara.
Sela
 
Sa’an nan na furta zunubina a gare ka
ban kuwa ɓoye laifina ba.
Na ce, “Zan furta
laifofina ga Ubangiji.”
Ka kuwa gafarta
laifin zunubina.
Sela
 
Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka
yayinda kake samuwa;
tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso,
ba za su kai wurinsa ba.
Kai ne wurin ɓuyata;
za ka tsare ni daga wahala
ka kewaye ni da waƙoƙin ceto.
Sela
 
Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi;
Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.
Kada ka zama kamar doki ko doki,
wanda ba su da azanci
wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama
in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba.
10 Azaban mugu da yawa suke,
amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa
kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.
 
11 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai;
ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai!
* Zabura 32: Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce.