*
Zabura 34
Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi.
Zan gode wa Ubangiji kullayaumi;
yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.
Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji;
bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.
Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni;
bari mu ɗaukaka sunansa tare.
 
Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini;
ya cece ni daga dukan tsoro.
Waɗanda suke dubansa sukan haskaka;
fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.
Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi;
ya cece shi daga dukan wahalarsa.
Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,
ya kuwa cece su.
 
Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;
mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.
Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa,
gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.
10 Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa,
amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.
11 Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni;
zan koya muku tsoron Ubangiji.
12 Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa
yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,
13 ka kiyaye harshenka daga mugunta
da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.
14 Juyo daga mugunta ku yi alheri;
nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.
 
15 Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci
kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;
16 fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta,
don yă sa a manta da su a duniya.
 
17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;
yakan cece su daga dukan wahalarsu.
18  Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai
ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
 
19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa,
amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;
20 yakan tsare dukan ƙasusuwansa,
ba ko ɗayansu da zai karye.
 
21 Mugunta zai kashe mugu;
za a hukunta abokan gāban adalai.
22  Ubangiji yakan cece bayinsa;
ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.
* Zabura 34: Wannan zabura waƙa ce, mai ayoyin da suka fara da harufan Ibraniyanci bi da bi.