Zabura 39
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zabura ta Dawuda.
Na ce, “Zan lura da hanyoyina
zan kuma kiyaye harshena daga zunubi;
zan sa linzami a bakina
muddin mugaye suna a gabana.”
Na yi shiru, ban ce kome ba,
Ko a kan abin da yake da kyau!
Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi;
zuciyata ta ƙara zafi a cikina.
Kuma sa’ad da nake tunani, wuta ta yi ta kuna;
sai na yi magana da harshena na ce,
 
“Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata
da kuma yawan kwanakina;
bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri.
Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai;
yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka.
Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum,
har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya.
Sela
 
“Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa.
Yana ta yawo, amma a banza ne kawai;
yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba.
 
“Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema?
Begena yana a gare ka.
Ka cece ni daga dukan laifofina;
kada ka sa in zama abin dariya ga wawaye.
Na yi shiru; ba zan buɗe bakina ba,
gama kai ne wanda ka aikata wannan.
10 Ka ɗauke bulalarka daga gare ni;
na ji jiki ta wurin bugun da hannunka ya yi mini.
11 Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu;
kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi,
kowane mutum dai shaƙar iska ne.
Sela
 
12 “Ka ji addu’ata, ya Ubangiji,
ka saurari kukata ta neman taimako;
kada ka kurmance ga kukata.
Gama ina zama tare da kai kamar baƙo,
baƙo, kamar yadda dukan kakannina sun kasance.
13 Ka kau da fuskarka daga gare ni, saboda in sāke yin farin ciki
kafin in tafi in kuma rabu da nan.”