Zabura 41
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi;
Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.
Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa;
zai albarkace shi a cikin ƙasar
ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.
Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa
ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.
 
Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai;
ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”
Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa,
“Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?”
Duk sa’ad da wani ya zo ganina,
yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi;
sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.
 
Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina;
suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,
“Mugun ciwo ya kama shi;
ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”
Har abokina na kurkusa,
wanda na amince da shi,
wanda muke cin abinci tare,
ya juya yana gāba da ni.
 
10 Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai,
ka tā da ni, don in sāka musu.
11 Na sani kana jin daɗina,
gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba.
12 Cikin mutuncina ka riƙe ni
ka sa ni a gabanka har abada.
 
 
13 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,
har abada abadin.
Amin kuma Amin.