Zabura 49
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce.
Ku ji wannan, dukanku mutane;
ku saurara, dukanku waɗanda suke zama a wannan duniya,
babba da yaro
mai arziki da talaka.
Bakina zai yi maganar hikima;
magana daga zuciyata za tă ba da ganewa.
Zan juye kunnena ga karin magana;
da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina.
 
Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo,
sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni,
waɗanda suka dogara ga arzikinsu
suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu?
Ba wani da zai iya ceton ran wani
ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,
kuɗin fansa domin rai yana da tsada,
babu abin da za a biya da ya taɓa isa,
da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada
yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.
10 Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa;
wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka
su bar wa waɗansu arzikinsu.
11 Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada,
Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa,
ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
 
12 Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama;
shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
 
13 Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu,
da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu.
Sela
14 Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari;
za su kuwa zama abincin mutuwa
amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe.
Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari,
nesa da gidajensu masu tsada.
15 Amma Allah zai ceci raina daga kabari;
tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa.
Sela
16 Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki
sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru;
17 gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba,
darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba.
18 Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne,
mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,
19 zai gamu da tsarar kakanninsa,
waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.
 
20 Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba
shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.