Zabura 51
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba.
Ka yi mini jinƙai, ya Allah,
bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa;
bisa ga tausayinka mai girma
ka shafe laifofina.
Ka wanke dukan kurakuraina
ka tsarkake ni daga zunubina.
 
Gama ina sane da laifofina
zunubaina kuma kullum suna a gabana.
Kai kaɗai na yi wa zunubi
na yi abin da yake mugu a idonka,
ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana
aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.
Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa
mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.
Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki;
ka koya mini hikima a wuri can ciki.
 
Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab;
ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.
Bari in ji farin ciki da murna;
bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.
Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina
ka kuma shafe dukan kurakuraina.
 
10 Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah,
ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.
11 Kada ka fid da ni daga gabanka
ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.
12 Ka mayar mini farin cikin cetonka
ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.
 
13 Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka,
masu zunubi kuma za su komo gare ka.
14 Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah,
Allahn da ya cece ni,
harshena kuwa zai rera adalcinka.
15 Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana,
bakina kuwa zai furta yabonka.
16 Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo;
ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.
17 Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu;
karyayyiya da kuma zuciya mai tuba,
Ya Allah, ba za ka ƙi ba.
 
18 Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara;
ka gina katangar Urushalima.
19 Ta haka za a kasance da hadayu masu adalci,
hadayun ƙonawa ɗungum don su faranta ka;
sa’an nan za a miƙa bijimai a bagadenka.