Zabura 70
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Roƙo.
Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni;
Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni.
 
Bari masu neman raina
su sha kunya su kuma rikice;
bari dukan masu sha’awar gani lalacewata
su juye baya da kunya.
Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!”
Su juye baya saboda kunyansu.
Amma bari dukan masu nemanka
su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka;
bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce,
“Bari Allah yă sami ɗaukaka!”
 
Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata;
ka zo da sauri gare ni, ya Allah.
Kai ne mai taimakona da mai cetona;
Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri.