Zabura 72
Ta Solomon.
Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah,
ɗan sarki da adalcinka.
Zai* shari’anta mutanenka da adalci,
marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.
 
Duwatsu za su kawo wadata ga mutane,
tuddai kuma su ba da amfani na adalci.
Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane
yă kuma cece ’ya’yan masu bukata;
zai murƙushe masu danniya.
Zai jimre muddin rana tana nan,
muddin akwai wata, har dukan zamanai.
Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka,
kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
A kwanakinsa adalai za su haɓaka
wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.
 
Zai yi mulki daga teku zuwa teku
kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya.
Kabilun hamada za su rusuna a gabansa
abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.
10 Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa
za su ba da gandu gare shi;
sarakunan Sheba da Seba
za su ba shi kyautai.
11 Dukan sarakuna za su rusuna masa
kuma dukan al’ummai za su bauta masa.
 
12 Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka,
marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.
13 Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata
yă ceci masu bukata daga mutuwa.
14 Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici,
gama jininsu yake a gabansa.
 
15 Bari yă yi doguwar rayuwa!
Bari a ba shi zinariya daga Sheba.
Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa
su kuma albarkace shi dukan yini.
16 Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar;
bari yă cika bisan tuddai.
Bari ’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon;
bari yă bazu kamar ciyayi a gona.
17 Bari sunansa yă dawwama har abada;
bari yă ci gaba muddin rana tana nan.
 
Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa,
za su kuma ce da shi mai albarka.
 
 
18 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila,
wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki.
19 Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada;
bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa.
Amin kuma Amin.
 
 
20 Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse.
* Zabura 72:2 Ko kuwa Bari yă; daidai da ayoyi 3-11 da kuma 17. Zabura 72:8 Wato, Yuferites Zabura 72:8 Ko kuwa iyakar ƙasa