Zabura 92
Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci.
Yana da kyau a yabi Ubangiji
a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
don a yi shelar ƙaunarka da safe
amincinka kuma da dare,
da kiɗin molo mai tsirkiya goma
da kuma ƙarar garaya.
 
Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji;
na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.
Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji,
tunaninka da zurfi suke ƙwarai!
Mutum marar azanci ba zai sani ba,
wawa ba zai gane ba,
cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa
kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka,
za a hallaka su har abada.
 
Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.
 
Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji,
tabbatacce abokan gābanka za su hallaka;
za a watsar da dukan masu aikata mugunta.
10 Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna;
an zubo mai masu kyau a kaina.
11 Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana;
kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.
 
12 Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino,
za su yi girma kama al’ul na Lebanon;
13 da aka daddasa a gidan Ubangiji,
za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.
14 Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu,
za su kasance ɗanye kuma kore shar,
15 suna shela cewa, “Ubangiji adali ne;
shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”