12
Jarumawa sun haɗa kai da Dawuda
Waɗannan su ne mutanen da suka zo wurin Dawuda a Ziklag, yayinda aka kore shi daga gaban Shawulu ɗan Kish (suna cikin jarumawan da suka taimake shi a yaƙi; suna da baka suna kuma iya harba kibiya, ko majajjawa da hannun dama ko na hagu; su ’yan’uwan Shawulu ne daga kabilar Benyamin):
 
Ahiyezer babbansu da Yowash ’ya’yan Shema’a maza daga Gibeya;
Yeziyel da Felet ’ya’yan Azmawet;
Beraka, Yehu daga Anatot, da Ishmahiya daga Gibeyon, wani jarumi a cikin Talatin nan, wanda shi ne shugaban Talatin;
Irmiya, Yahaziyel, Yohanan, Yozabad daga Gedera, Eluzai, Yerimot, Beyaliya, Shemariya da Shefatiya daga Haruf;
Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezer da Yashobeyam daga Kora;
da Yoyela da Zebadiya ’ya’yan Yeroham maza daga Gedor.
 
Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu.
 
Ezer shi ne babba,
Obadiya shi ne mai binsa a shugabanci, Eliyab na uku,
10 Mismanna na huɗu, Irmiya na biyar,
11 Attai na shida, Eliyel na bakwai,
12 Yohanan na takwas, Elzabad na tara,
13 Irmiya na goma da kuma Makbannai na goma sha ɗaya.
 
14 Waɗannan mutanen Gad shugabannin mayaƙa ne; ƙarami a cikinsu zai iya ƙara da mutum ɗari, kuma babba a cikin zai iya ƙara da dubu. 15 Su ne suka haye Urdun a wata na farko sa’ad da kogin ya yi ambaliya, suka kuma kori duk mai rai a kwarin, na wajen gabas da na wajen yamma.
16 Sauran mutanen Benyamin da waɗansu mutanen Yahuda su ma suka zo wurin Dawuda a kagararsa. 17 Sai Dawuda ya fita don yă tarye su, ya kuma ce musu, “In kun zo wurina da salama, don ku taimake ni, to, ina a shirye in bar ku ku haɗa kai tare da ni. Amma in kun zo don ku bashe ni ga abokan gābana sa’ad da hannuwana ba su da laifi a rikici, bari Allah na kakanninmu yă duba yă kuma shari’anta ku.”
18 Sai Ruhu ya sauko a kan Amasai, shugaban Talatin nan, sai ya ce,
“Mu naka ne, ya Dawuda!
Muna tare da kai, ya ɗan Yesse!
Nasara, nasara gare ka,
nasara kuma ga waɗanda suke taimakonka.
Gama Allahnka zai taimake ka.”
Saboda haka Dawuda ya karɓe su ya kuma mai da su shugabannin ƙungiyoyin maharansa.
19 Waɗansu mutanen Manasse suka haɗa kai da Dawuda sa’ad da ya tafi tare da Filistiyawa don yă yaƙi Shawulu (Shi da mutanensa ba su taimaki Filistiyawa ba domin bayan shawarwari, shugabanninsu suka salame shi. Sun ce, “Za mu biya da kawunanmu in ya koma ga maigidansa Shawulu.”) 20 Da Dawuda ya tafi Ziklag, waɗannan mutanen Manasse ne suka haɗa kai da shi. Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika’ilu, Yozabad, Elihu da Zilletai, shugabannin ƙungiyoyi na dubu a cikin Manasse. 21 Suka taimaki Dawuda a kan ƙungiyoyin hari, gama dukansu jarumawa ne sosai, kuma su shugabanni ne a cikin mayaƙansa. 22 Kowace rana mutane suka riƙa zuwa don su taimaki Dawuda, sai da ya kasance da runduna mai girma, kamar mayaƙan Allah.
Saura sun haɗa kai da Dawuda a Hebron
23 Ga yawan mutanen shiryayyu don yaƙi waɗanda suka zo wurin Dawuda a Hebron don su mai da mulkin Shawulu gare shi, yadda Ubangiji ya faɗa.
 
24 Mutanen Yahuda, masu riƙe garkuwa da māshi, su 6,800 shiryayyu don yaƙi;
25 mutanen Simeyon, jarumawa shiryayyu don yaƙi, su 7,100;
26 mutanen Lawi, su 4,600, 27 haɗe da Yehohiyada, shugaban iyalin Haruna tare da mutane 3,700, 28 da Zadok, matashi jarumi sosai, tare da shugabanni su 22 daga iyalinsa;
29 mutanen Benyamin, ’yan’uwan Shawulu, su 3,000, yawanci waɗanda suke biyayya ga gidan Shawulu sai lokacin;
30 mutanen Efraim, jarumawa, sanannu cikin gidajensu, su 20 800;
31 mutanen rabin kabilar Manasse, sanannu da sunaye suka zo suka mai da Dawuda sarki, su 18,000;
32 mutanen Issakar, masu fahimtar lokuta suka kuma san abin da ya kamata Isra’ila ya yi, manya 200, tare da danginsu a ƙarƙashin shugabancinsu;
33 mutanen Zebulun, ƙwararru sojoji shiryayyu don yaƙi da kowane irin makami, suka zo don su taimaki Dawuda da zuciya ɗaya, su 50,000;
34 mutanen Naftali su 1,000 shugabanni, tare da mutane 37,000 masu riƙe garkuwa da masu;
35 mutanen Dan, shiryayyu don yaƙi, su 28,600;
36 mutanen Asher, ƙwararrun sojoji shiryayyu don yaƙi, su 40,000;
37 kuma daga gabashin Urdun, mutanen Ruben, Gad da kuma rabin kabilar Manasse, masu kayan yaƙi iri-iri, su 120,000.
 
38 Dukan waɗannan mayaƙa ne waɗanda suka ba da kansu da yardar rai su yi hidima.
 
Suka zo Hebron da cikakken niyya don su naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila. Duka sauran Isra’ilawa su ma suka goyi baya a naɗa Dawuda sarki. 39 Mutanen suka yi kwana uku a can tare da Dawuda, suna ci suna sha, gama iyalansu sun yi musu tanadi. 40 Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun ’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.