21
Dawuda ya ƙidaya mayaƙansa
(2 Sama’ila 24.1-9)
1 Sai Shaiɗan ya tashi gāba da Isra’ila, ya zuga Dawuda ya ƙidaya Isra’ila.
2 Saboda haka Dawuda ya ce wa Yowab da shugabannin mayaƙa, “Ku tafi ku ƙidaya Isra’ilawa daga Beyersheba zuwa Dan. Ku kawo mini labarin saboda in san su nawa ne.”
3 Amma Yowab ya amsa ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya mayaƙansa fiye da sau ɗari. Ranka yă daɗe sarki, dukansu ba bayin shugabana ba ne? Me ya sa ranka yă daɗe yake so yă yi haka? Me zai sa ka kawo laifi a kan Isra’ila?”
4 Amma sarki ya nace a kan maganar da ya yi wa Yowab. Sai Yowab ya tashi ya tafi cikin dukan Isra’ila, ya kewaye sa’an nan ya dawo Urushalima.
5 Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. A cikin Isra’ila akwai mutum miliyon da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su iya riƙe takobi, haɗe da dubu ɗari huɗu da saba’in a Yahuda.
6 Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba.
(2 Sama’ila 24.10-17)
7 Wannan umarnin mugu ne a gaban Allah; saboda haka ya hukunta Isra’ila.
8 Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai ta wurin yin wannan. Yanzu, na roƙe ka, ka ɗauke laifin bawanka. Na yi wauta sosai.”
9 Sai Ubangiji ya ce wa Gad, mai duba na Dawuda,
10 “Tafi ka faɗa wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina ba ka abubuwa uku. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu don in aikata a kanka.’ ”
11 Saboda haka Gad ya tafi wurin Dawuda ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka yi zaɓi,
12 shekara uku na yunwa, wata uku na shan ɗibga a gaban abokan gābanka, sa’ad da za su bi suna kakkashe ku, ko kuwa kwana uku na takobin Ubangiji, ranakun annoba a cikin ƙasar, mala’ikan Ubangiji zai hallaka kowane sashe na Isra’ila.’ Yanzu sai ka yanke shawara yadda zan amsa wa wanda ya aiko ni.”
13 Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Bari in fāɗa a hannuwan Ubangiji, gama jinƙansa yana da girma sosai; amma kada ka bari in fāɗa a hannuwan mutane.”
14 Sai Ubangiji ya aiko da annoba a kan Isra’ila, mutane duba saba’in na Isra’ila suka mutu.
15 Allah kuwa ya aiki mala’ika yă hallaka Urushalima. Amma yayinda mala’ikan yana gab da yin haka, sai Ubangiji ya gani ya kuma yi nadama saboda masifar, sai ya ce wa mala’ikan wanda yake hallaka mutane, “Ya isa! Janye hannunka.” Mala’ikan Ubangiji kuwa yana tsaye a masussukar Ornan mutumin Yebus.
16 Sai Dawuda ya ɗaga ido ya ga mala’ikan Ubangiji tsaye tsakanin sama da duniya, da takobi a zāre a hannunsa ya miƙa a kan Urushalima. Sai Dawuda da dattawa, saye da rigunan makoki suka fāɗi rubda jiki.
17 Dawuda ya ce wa Allah, “Ba ni ba ne na umarta a ƙidaya mayaƙan? Ni ne wanda ya yi zunubin da kuma abin da ba daidai ba. Waɗannan dai tumaki ne. Me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, bari hannunka ya fāɗi a kaina da kuma iyalina, amma kada ka bar wannan annoba ya kasance a kan mutanenka.”
(2 Sama’ila 24.18-25)
18 Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya umarci Gad yă faɗa wa Dawuda yă haura yă gina bagade wa Ubangiji a masussukar Ornan mutumin Yebus.
19 Saboda haka Dawuda ya haura cikin biyayya ga maganar da Allah ya yi da sunan Ubangiji.
20 Yayinda Ornan yake sussukar alkama, sai ya juya ya ga mala’ika; ’ya’yansa maza guda huɗu da suke tare da shi suka ɓuya.
21 Sai Dawuda ya kusato, sa’ad da Ornan ya duba sai ya gan shi, ya bar masussukar ya rusuna a gaban Dawuda da fuskarsa har ƙasa.
22 Dawuda ya ce wa Ornan, “Ka ba ni masussukarka saboda in gina bagade wa Ubangiji, don annobar da take kan mutane tă daina. Ka sayar mini ita a cikakken kuɗinta.”
23 Ornan ya ce wa Dawuda, “Ka karɓa! Bari ranka yă daɗe, sarki yă yi duk abin da ya ga ya yi masa kyau. Duba, zan ba da shanu domin hadaya ta ƙonawa, da itacen sussuka, da kuma alkama domin hadaya ta gari. Zan ba da dukan wannan.”
24 Amma Sarki Dawuda ya amsa wa Ornan ya ce, “A’a, na nace zan biya cikakken kuɗinta. Ba zan karɓi abinka kawai don Ubangiji ba, ko in miƙa hadaya ta ƙonawar da ba tă ci mini wani abu ba.”
25 Saboda haka Dawuda ya biya Ornan shekel ɗari shida na zinariya saboda wurin.
26 Dawuda ya gina bagade wa Ubangiji a can ya kuma miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wuta daga sama a kan bagaden hadaya ta ƙonawa.
27 Sa’an nan Ubangiji ya yi magana ga mala’ikan, ya kuma mayar da takobinsa a kube.
28 A lokacin, sa’ad da Dawuda ya ga cewa Ubangiji ya amsa masa a masussukar Ornan mutumin Yebus, sai ya miƙa hadayu a can.
29 Tabanakul na Ubangiji da Musa ya yi a hamada, da kuma bagaden hadaya ta ƙonawa a lokacin suna a tudun Gibeyon.
30 Amma Dawuda bai iya zuwa gabansa don yă yi tambaya ga Allah ba, gama yana jin tsoron takobin mala’ikan Ubangiji.