24
Sassan firistoci
1 Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza.
’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
2 Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci.
3 Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima.
4 Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar.
5 Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.
6 Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.
7 Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib,
na biyu a kan Yedahiya,
8 na uku a kan Harim,
na huɗu a kan Seyorim,
9 na biyar a kan Malkiya,
na shida a kan Miyamin,
10 na bakwai a kan Hakkoz,
na takwas a kan Abiya,
11 na tara a kan Yeshuwa,
na goma a kan Shekaniya,
12 na goma sha ɗaya a kan Eliyashib,
na goma sha biyu a kan Yakim,
13 na goma sha uku a kan Huffa,
na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab,
14 na goma sha biyar a kan Bilga,
na goma sha shida a kan Immer,
15 na goma sha shida a kan Hezir,
na goma sha takwas a kan Haffizzez,
16 na goma sha tara a kan Fetahahiya,
na ashirin a kan Ezekiyel,
17 na ashirin da ɗaya wa Yakin,
na ashirin da biyu a kan Gamul,
18 na ashirin da uku wa Delahiya
da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya.
19 Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi.
Sauran Lawiyawa
20 Game da sauran zuriyar Lawi kuwa,
Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel;
daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya.
21 Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.
22 Daga mutanen Izhar, Shelomot;
daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat.
23 ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
24 Ɗan Uzziyel shi ne, Mika;
daga ’ya’yan Mika maza, Shamir.
25 Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya;
daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya.
26 ’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi.
Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno.
27 ’Ya’yan Merari su ne,
daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri.
28 Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza.
29 Daga Kish, ɗan Kish shi ne,
Yerameyel.
30 Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot.
Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu.
31 Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.