10
Isra’ila ya yi tawaye a kan Rehobowam
(1 Sarakuna 12.1-20)
Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ilawa sun je can don su naɗa shi sarki. Da Yerobowam ɗan Nebat ya ji wannan (a lokacin yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon ya tafi), sai ya dawo daga Masar. Saboda haka suka aika a zo da Yerobowam, sai shi da dukan Isra’ila suka je wurin Rehobowam suka ce masa. “Mahaifinka ya sa mana kaya masu nauyi a kanmu, amma yanzu ka sauƙaƙa mana aiki mai zafin nan da kuma kaya masu nauyin da ya sa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
Rehobowam ya amsa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.” Saboda haka mutanen suka watse.
Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawan da suka yi wa mahaifinsa Solomon hidima a lokacin da yake da rai, ya tambaye suya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?”
Suka amsa suka ce, “In za ka ji tausayi waɗannan mutane ka kuma gamshe su, ka kuma ba su amsar da ta dace, kullum za su zama bayinka.”
Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawa suka ba shi ya kuma nemi shawarar matasan da suka yi girma tare, suke kuma yin masa hidima. Ya tambaye su ya ce, “Mece ce shawararku? Yaya zan amsa wa waɗannan mutanen da suke ce mini, ‘Ka sauƙaƙa nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?”
10 Matasan da suka yi girma tare shi suka amsa, “Faɗa wa mutanen da suke ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sauƙaƙa nauyinmu.’ Ka faɗa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun mahaifina kauri. 11 Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.’ ”
12 Bayan kwana uku sai Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam, yadda sarki ya ce, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.” 13 Sarki ya amsa musu da kakkausar murya. Ya ƙi shawarar dattawan, 14 ya kuma bi shawarar matasan ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.” 15 Saboda haka sarki bai saurari mutane ba, gama wannan juyin al’amura daga Allah ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi ga Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya mutumin Shilo.
16 Sa’ad da Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, suka ce,
“Wanda rabo muke da shi a wurin Dawuda,
wanda sashe muke da shi daga ɗan Yesse?
Kowa yă koma tentinsa, ya Isra’ila!
Ka lura da gidanka, ya Dawuda!”
Saboda haka dukan Isra’ilawa suka tafi gida. 17 Amma game da Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da yin mulki a bisansu.
18 Sarki Rehobowam ya aiki Hadoram wanda yake lura da aikin dole, amma Isra’ilawa suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta ya shiga keken yaƙinsa ya gudu zuwa Urushalima. 19 Ta haka Isra’ila ya kasance cikin tawaye a kan gidan Dawuda har yă zuwa wannan rana.