13
Abiya sarkin Yahuda
(1 Sarakuna 15.1-8)
A shekara ta sha takwas ta sarautar Yerobowam, Abiya ya zama sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru uku. Sunan mahaifiyarsa Mikahiya ce, ’yar Uriyel na Gibeya.
Aka kasance da yaƙe-yaƙe tsakanin Abiya da Yerobowam. Abiya ya tafi yaƙi tare da mayaƙa dubu ɗari huɗu jarumawa, Yerobowam kuwa ya ja dāgār yaƙi a kan Abiya da mayaƙa dubu ɗari takwas jarumawa.
Abiya ya tsaya a Dutsen Zemarayim, a ƙasar tudu ta Efraim ya ce, “Yerobowam da dukan Isra’ila, ku saurare ni! Ba ku san cewa Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ba da sarautar Isra’ila ga Dawuda da zuriyarsa har abada ta wurin alkawarin gishiri ba? Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, ma’aikacin Solomon ɗan Dawuda, ya tayar wa maigidansa, sai ya tara wa kansa ’yan iska da mugayen mutane suka yi gāba da Rehobowam ɗan Solomon. Rehobowam lokacin kuwa ba shi da wayo, don haka bai iya tsai da su ba.
“Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku. Ba ku ne kuka kori firistocin Ubangiji, ’ya’yan Haruna maza, da Lawiyawa kuka kuma zaɓi firistocinku kamar yadda sauran al’ummai suke yi ba? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don yă tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.
10 “Gare mu kuwa, Ubangiji shi ne Allah, kuma ba mu yashe shi ba. Firistocin da suke bauta wa Ubangiji ’ya’yan Haruna maza ne, Lawiyawa ne kuwa suke taimakonsu. 11 Kowace safiya da kowace yamma sukan miƙa hadayun ƙonawa da turare mai ƙanshi ga Ubangiji. Sukan shirya burodi a tsarkaken tebur mai tsabta, sukan kuma ƙuna fitilu a alkukai kowace yamma. Muna kiyaye ƙa’idodin Ubangiji Allahnmu. Amma ku kun yashe shi. 12 Allah yana tare da mu; shi ne shugabanmu. Firistocinsa tare da ƙahoni za su busa kirarin yaƙi a kanku. Mutanen Isra’ila, kada ku yi yaƙi da Ubangiji Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”
13 To, fa, Yerobowam ya aiki mayaƙa su zagaya daga baya, domin yayinda yake a gaban Yahuda, sai ’yan kwanto su kasance a bayansu. 14 Yahuda ya juya sai ya ga cewa ana yaƙe su gaba da baya. Sai suka yi kuka ga Ubangiji. Firistoci suka busa ƙahoni 15 mutanen Yahuda kuwa suka tā da kirarin yaƙi. Da ji kirarin yaƙi, Allah ya fatattake Yerobowam da dukan Isra’ila a gaban Abiya da Yahuda. 16 Isra’ilawa suka gudu a gaban Yahuda, Allah kuwa ya bashe su a hannuwansu. 17 Abiya da mutanensa suka kashe su sosai, har mutum dubu ɗari biyar suka mutu a cikin jarumawan Isra’ila. 18 Aka cinye mutanen Isra’ila a wannan lokaci, mutanen Yahuda kuwa suka yi nasara domin sun dogara ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
19 Abiya ya kori Yerobowam ya kuma ƙwace garuruwan Betel, Yeshana da Efron, tare da ƙauyukan da suke kewaye daga gare shi. 20 Yerobowam bai sāke yin ƙarfi a zamanin Abiya ba. Ubangiji ya buge shi ya kuma mutu.
21 Amma Abiya ya ƙara ƙarfi. Ya auri mata goma sha huɗu, ya kuma kasance da ’ya’ya maza ashirin da biyu da kuma ’ya’ya mata goma sha shida.
22 Sauran ayyukan sauratar Abiya, abin da ya yi da abin da ya faɗa, a rubuce suke a cikin rubuce-rubucen annabi Iddo.