27
Yotam sarkin Yahuda
(2 Sarakuna 15.32-38)
Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda mahaifinsa Uzziya ya yi, sai dai bai kutsa cikin haikalin Ubangiji kamar mahaifinsa ba. Mutane kuwa, suka ci gaba da aikata ayyukan lalaci. Yotam ya sāke ginin Ƙofar Bisa na haikalin Ubangiji, ya kuma yi aiki sosai a katanga a tudun Ofel. Ya gina garuruwa a tuddan Yahuda, ya giggina katanga da gine-gine masu tsawo a wuraren da suke a kurmi.
Yotam ya yi yaƙi da sarkin Ammonawa ya kuma ci su. A wannan shekara Ammonawa suka biya shi haraji talenti ɗari na azurfa, garwan alkama dubu goma da kuma garwa dubu goma na sha’ir. Ammonawa suka kawo masa wannan kuma a shekara ta biyu da ta uku.
Yotam ya ƙaru a iko saboda ya daidaita al’amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa.
Sauran ayyuka a mulkin Yotam, haɗe da dukan yaƙe-yaƙensa da waɗansu abubuwan da ya yi, suna a rubuce a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.