4
Kayayyakin haikalin
(1 Sarakuna 7.23-51)
Ya yi bagaden tagulla mai tsawo kamu ashirin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu goma. Ya yi ƙaton kwano mai suna Teku na zubin ƙarfe, mai siffar da’ira, awonsa kamu goma ne daga da’ira zuwa da’ira tsayinsa kuma kamu biyar. Ya ɗauki magwaji mai tsawo kamu talatin ya auna shi kewaye. Ƙasa da da’ira kuwa, akwai siffofin bijimai kewaye da ita, goma ga kowane kamu guda. An yi zubin bijiman a jeri biyu a gefe guda na kwatarniya.
Tekun ya tsaya a kan bijimai goma sha biyu, uku na fuskantar arewa, uku na fuskantar yamma, uku na fuskantar kudu, uku kuma na fuskantar gabas. Tekun ya zauna a kansu, kuma ƙarfafun bayansu suna wajen tsakiya. Kaurin ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kama da’irar kwaf, kama furen da ya tohu. Ya riƙe randuna dubu uku.
Sa’an nan ya yi daruna goma don wanki ya sa biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. A cikinsu kayan da za a yi amfani don ɗauraye hadayun ƙonawa, amma firistoci suna amfani da ƙaton kwano mai suna Teku don wanki.
Ya yi wurin ajiye fitila goma na zinariya bisa ga tsari dominsu ya kuma sa su a haikali, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa.
Ya yi tebur goma ya kuma sa su cikin haikalin, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. Ya kuma yi kwanonin yayyafawa guda ɗari.
Ya yi fili na firistoci da kuma babban fili da ƙofofi domin filin, ya shafe ƙofofin da tagulla. 10 Ya sa ƙaton kwano mai suna Teku a gefen kudu, a kusurwa kudu maso gabas.
11 Ya kuma yi tukwane da manyan cokula da kwanonin yayyafawa.
Ta haka Huram ya gama aikin da ya yi wa Sarki Solomon a cikin haikalin Allah.
 
12 Ginshiƙai biyu;
kwanoni biyu masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai;
jeri biyu na tuƙaƙƙen adon kwanonin yayyafawa masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai;
13 rumman ɗari huɗu don jeri biyu na tuƙaƙƙe (layi biyu na rumman don kowane tuƙaƙƙe, mai adon kwano mai siffar kwartaniya a bisan ginshiƙai);
14 dakalai da darunansu;
15 ya yi kwanon da ya kira Teku, da bijimai goma sha biyu a ƙarƙashinsa;
16 tukwane, manyan cokula, cokula masu yatsu don nama da dukan kayayyakin da suka shafi wannan.
 
Dukan kayayyakin da Huram-Abi ya yi domin Sarki Solomon saboda haikalin Ubangiji an yi su da gogaggen tagulla ne. 17 Sarki ya sa aka yi zubinsu a katakon yin tubali a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zereda. 18 Dukan waɗannan abubuwa da Solomon ya yi suna da tsada ƙwarai har suka kai nauyin tagullar da ya fi misali.
19 Solomon ya kuma yi dukan kayayyakin da suke a cikin haikalin Allah.
 
Bagaden zinariya;
teburin da ake ajiye burodin Kasancewa;
20 wurin ajiye fitila na zinariya zalla tare da fitilunsu, don ƙonawa a gaban wuri mai tsarki na ciki kamar yadda aka tsara;
21 aikin zānen furannin zinariya da fitilu da abin ɗiban wuta (an yi su da zinariya zalla);
22 arautaki; kwanonin yayyafawa, kwanoni da hantsuka; da kuma ƙofofin zinariya na haikali, ƙofofi na ciki zuwa Wuri Mafi Tsarki da kuma ƙofofin babban zaure.