22
Dawuda a Adullam da Mizfa
Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da ’yan’uwansa da kuma iyalan mahaifinsa suka ji labari, sai suka tafi can wurinsa. Dukan mutanen da suke cikin wahala, da waɗanda ake binsu bashi, da masu damuwoyi, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Yawansu ya kai ɗari huɗu.
Daga can Dawuda ya tafi Mizfa a Mowab. Ya ce wa sarkin Mowab, “Za ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Allah zai yi da ni?” Saboda haka ya bar su a wurin sarkin Mowab, suka zauna da shi duk tsawon lokacin da Dawuda yake ta ɓuya a kogwannin duwatsu.
Amma annabin nan Gad ya ce wa Dawuda, “Kada ka zauna a nan, maza ka tashi ka shiga ƙasar Yahuda”. Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Heret.
Shawulu ya kashe firistocin Nob
Sai Shawulu ya sami labari cewa an ga Dawuda da mutanensa. Shawulu kuwa yana zaune da māshinsa kusa a ƙarƙashin itacen tsamiya a tudun Gibeya, tare da dukan ma’aikatansa kewaye da shi. Ya ce musu, “Mutanen Benyamin, ku saurara; ɗan Yesse zai iya ba dukanku filaye da gonakin inabi ne? Zai ba dukanku shugabanci na dubbai ko shugabanci na ɗari-ɗari? Abin da ya sa dukanku kuka gama baki a kaina? Ba wanda ya gaya mini lokacin da ɗana ya yi yarjejjeniya da ɗan Yesse, ba wanda ya kulla da ni, ko ya gaya mini cewa ɗana ya sa bawana yă tayar mini, yana fakona kamar yadda yake a yau.”
Amma Doyeg mutumin Edom da yake tsaye tare da fadawan Shawulu ya ce, “Na ga ɗan Yesse ya zo wurin Ahimelek ɗan Ahitub a Nob. 10 Ahimelek ya roƙi Ubangiji saboda shi, ya kuma ba shi guzuri da takobin Goliyat Bafilistin.”
11 Sai sarki ya aika aka kira masa Ahimelek firist ɗan Ahitub da dukan iyalin mahaifinsa. Dukansu suka zo wurin sarki. 12 Shawulu ya ce, “Ka saurara yanzu, ɗan Ahitub.”
Ya amsa ya ce, “Ina saurara, ranka yă daɗe.”
13 Shawulu ya ce masa, “Don me ka gama baki da ɗan Yesse a kaina har ka ba shi burodi da takobin (Goliyat), ka kuma roƙi Allah don yă tayar mini, yă kuma yi fakona kamar yadda yake yi yau?”
14 Ahimelek ya ce wa sarki, “A cikin bayinka duka, wa ke da aminci iri na Dawuda, surukin sarki, shugaban jarumanka wanda ake girmamawa da gaske a gidanka? 15 A wannan rana ce da na fara roƙon Allah saboda shi? Kada sarki yă zargi bawansa ko wani daga iyalin mahaifinsa, gama bawanka bai san kome a kan dukan waɗannan al’amura ba.”
16 Amma sarki ya ce, “Lalle Ahimelek za ka mutu, da kai da dukan iyalin mahaifinka.”
17 Sai sarki ya umarci matsaran da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Ku kakkashe firistocin Ubangiji, gama su ma sun goyi bayan Dawuda. Sun san yana gudu, duk da haka ba su gaya mini ba.”
Amma ma’aikatan sarki ba su yarda su sa hannu su kashe firistocin Ubangiji ba.
18 Sai sarki ya umarce Doyeg ya ce, “Ka juya ka kakkashe firistocin.” Doyeg mutumin Edom ya juya ya kakkashe firistocin. A ranar kuwa ya kashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke sanye da efod na lilin. 19 Ya kuma hallaka Nob birnin firistoci, ya kashe dukan mata, da maza, da yara, da jarirai, da shanu, da jakuna, da kuma tumaki.
20 Amma Abiyatar ɗan Ahimelek jikan Ahitub ya tsere, ya gudu zuwa wurin Dawuda. 21 Abiyatar gaya wa Dawuda cewa, “Shawulu ya hallaka firistocin Ubangiji.” 22 Dawuda ya ce wa Abiyatar, “Lalle a wancan ranar, sa’ad da na ga Doyeg mutumin Edom a can, na san tabbatacce zai gaya wa sarki. Ni ne sanadin mutuwar dukan iyalin mahaifinka. 23 Ka zauna tare da ni, kada ka ji tsoro mutumin da yake neman ranka, yana nema raina ma. Ka zauna lafiya tare da ni.”