25
Dawuda da Nabal da Abigiyel
Sama’ila ya rasu, sai dukan Isra’ila suka taru suka yi makoki saboda shi. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya gangara zuwa cikin Jejin Faran.
A Mawon, akwai wani mutum wanda yake da dukiya a Karmel, mutumin mai arziki ne ƙwarai. Yana da awaki dubu ɗaya, da tumaki dubu uku waɗanda yake wa aski a Karmel. Ana ce da shi Nabal, sunan matarsa kuwa Abigiyel. Tana da hikima ga ta kuma kyakkyawa, amma mijinta mai rowa ne marar mutunci. Shi daga kabilar Kaleb ne.
Lokacin da Dawuda yake a jeji, ya ji labari cewa Nabal yana askin tumaki. Sai ya zaɓi samari goma ya aike su wurin Nabal a Karmel su gaishe shi a madadinsa, su ce masa, “Ranka yă daɗe, ina maka fatan alheri, kai da gidanka da dukan abin da kake da shi!
“Na ji cewa, yanzu lokacin askin tumaki ne. Sa’ad da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, kuma duk zamansu a Karmel ba abin da yake nasu da ya ɓata. Ka tambayi bayinka za su kuwa gaya maka. Saboda haka ka yi wa mutanena kirki, gama yau ranar biki ce. Ina roƙonka ka ba wa samarina, wato, bayinka, da ni ɗanka Dawuda, duk abin da kake iya ba su.”
Da mutanen Dawuda suka isa wurin Nabal, suka ba wa Nabal wannan saƙo a sunan Dawuda, sai suka jira.
10 Nabal ya ce wa mutanen Dawuda, “Wane ne wannan Dawuda? Wane ne wannan ɗan Yesse? Yawancin bayi suna tayar wa iyayengijinsu a kwanakin nan. 11 Don me zan ɗauki burodina da ruwana, da kuma naman da na yanka saboda masu yin wa tumakina aski in ba mutanen da ban ma san inda suka fito ba?”
12 Mutanen Dawuda suka juya suka koma. Da suka iso sai suka faɗa wa Dawuda abin da Nabal ya ce. 13 Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa yă rataya takobinsa.” Sai duk suka yi haka. Dawuda kuma ya rataya nasa. Mutum wajen ɗari huɗu suka tafi tare da Dawuda, mutum ɗari biyu kuwa suka zauna suna gadin kayansu.
14 Ɗaya daga cikin bayin Nabal ya gaya wa Abigiyel matar Nabal cewa, “Dawuda ya aiko da bayinsa daga jeji su gai da maigida, amma maigida ya zazzage su. 15 Waɗannan mutane kuwa sun yi mana kirki ƙwarai, ba su ba mu wata wahala ba. Babu abu guda da ya ɓace mana dukan lokacin da muke tare da su. 16 Dare da rana sun zama mana katanga kewaya da mu, a duk tsawon lokacin da muke kiwon tumakinmu kusa da su. 17 Ki yi nazari a kai, ki ga ko za ki iya yin wani abu, domin masifa yana nan rataye a wuyan maigidanmu da dukan iyalin gidansa. Shi mugun mutum ne wanda ba wani da zai iya yin masa magana.”
18 Abigiyel ba tă ɓata lokaci ba. Ta ɗauki burodi guda ɗari biyu, da salkar ruwan inabi biyu da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu biyar, da waina guda ɗari na ’ya’yan inabi, da masa ɗari biyu na kauɗar ɓaure ta labta wa jakuna. 19 Sai ta ce wa bawanta, “Yi gaba, zan bi ka”. Amma ba tă gaya wa Nabal, mijinta ba.
20 Da tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa suna gangarowa zuwa wajen da take. Sai ta tafi, ta sadu da su. 21 Bai daɗe ba da Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abinsa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta. 22 Bari Allah yă yi duk abin da ya ga dama da ni in na bar ko ɗaya daga mazan da suke da tare shi, gobe da safe.”
23 Da Abigiyel ta ga Dawuda, sai ta gaggauta ta sauka daga kan jaki, ta rusuna a gaban Dawuda da fuskarta har ƙasa. 24 Ta fāɗi a ƙafafunsa ta ce, “Bari laifin yă zama nawa, ranka yă daɗe. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka ji abin da baiwarka za tă ce. 25 Kada ranka yă daɗe, yă kula da Nabal, mugun mutumin nan. Shi dai kamar sunansa ne, sunansa Wawa ne, kuma wawanci yana cikinsa. Amma ni baiwarka, ban ga mutanen da ranka yă daɗe ya aika ba. 26 Da yake yanzu, ya mai girma, Ubangiji ya hana ka zubar da jini da kuma ɗaukan wa kanka fansa, muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, bari maƙiyinka da dukan waɗanda suke niyya su cuci shugabana su zama kamar Nabal. 27 Bari kuma ka karɓi wannan kyautar da baiwarka ta kawo don samarin da suke binka. 28 Ina roƙonka ka gafarta wa baiwarka laifinta gama tabbatacce Ubangiji zai ba shugabana dawwammamiyar sarauta, gama kana yin yaƙin Ubangiji ne. Kuma ba wani mugun abin da zai same ka muddin kana a raye. 29 Ko da yake wani mutum yana fafaranka domin yă kashe ka, Ubangiji Allahnka zai kiyaye ranka. Amma za a wurgar da rayukan maƙiyanka kamar yadda ake wurga dutsen majajjawa. 30 Sa’ad da Ubangiji ya cika kowane alherinsa da ya yi wa shugabana alkawari, ya kuma keɓe shi sarki a bisa Isra’ila, 31 kada yă zama cewa zuciyarka ta ba ka laifi ko ka damu cewa kana da alhakin jini, kada ka yi ramuwa da kanka. Sa’ad da Ubangiji ya nuna maka alheri, ka tuna da ni, baiwarka.”
32 Dawuda ya ce wa Abigiyel, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki don ki same ni yau. 33 Bari Allah yă albarkace ki saboda hikima yanke hukuncinki da kuma hana ni zubar da jini da ɗauka wa kaina fansa da hannuna a wannan rana. 34  Ubangiji, ya hana ni in yi miki ɓarna. Da ba don kin zo kin sadu da ni ba, na rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila Mai Rai, babu ko ɗaya daga cikin mazan gidan Nabal da zai rage gobe da safe.”
35 Sa’an nan Dawuda ya karɓi abin da ta kawo masa daga hannunta, ya kuma ce mata, “Ki koma gida kada ki damu, na ji koke-kokenki, zan kuma biya miki bukatarki.”
36 Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye. 37 Da safe sa’ad da Nabal ya natsu, sai matarsa ta gaya masa dukan abin da ya faru. Sai zuciyarsa ta tsinke, ya zama kamar dutse. 38 Bayan kusan kwana goma, Ubangiji ya bugi Nabal, sai ya mutu.
39 Da Dawuda ya sami labarin mutuwar Nabal, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya sāka mini a kan irin renin da Nabal ya yi mini. Ya hana bawansa yin mugunta, ga shi ya ɗora wa Nabal muguntar da ya yi.”
Sai Dawuda ya aika wa Abigiyel cewa tă zama matarsa. 40 Bayin Dawuda suka tafi Karmel suka ce wa Abigiyel, “Dawuda ya aike mu gare ki, mu zo mu ɗauke ki ki zama matarsa.”
41 Sai ta rusuna da fuskarta har ƙasa ta ce, “Ni baranyarka ce, na shirya in bauta maka in kuma wanke ƙafafun bayin shugabana.” 42 Abigiyel ta tashi da sauri ta hau jaki, ta kuma sa ’yan mata biyar da suke mata hidima su bi ta, suka tafi tare da ’yan saƙon Dawuda. Ta kuwa zama matarsa. 43 Dawuda a lokacin ya riga ya auri Ahinowam daga Yezireyel, dukansu suka zama matansa. 44 Amma Shawulu ya aurar da Mikal, ’yarsa, matar Dawuda, ga Falti ɗan Layish wanda yake daga Gallim.