8
Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila. Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyu kuwa Abiya. Suka yi alƙalanci a Beyersheba. Amma ’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya.
Sai dukan shugabannin Isra’ila suka taru suka zo wurin Sama’ila a Rama. Suka ce masa, “Ka tsufa, ’ya’yanka kuma ba sa bin hanyarka, saboda haka sai ka naɗa sarkin da zai bi da mu kamar yadda sauran ƙasashe suke da su.”
Amma Sama’ila bai ji daɗi sa’ad da suka ce, “Ka ba mu sarki da zai bi da mu.” Sai ya yi addu’a ga Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu. Haka suka yi daga tun daga ranar da na fitar da su daga Masar har zuwa yau, suka ƙi ni, suka bauta wa waɗansu alloli, haka ma suke yi maka. Yanzu ka saurare su amma ka yi musu kashedi sosai, ka sa su san abin da sarkin da zai bi da su zai yi.”
10 Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa. 11 Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe ’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa. 12 Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa. 13 Zai sa ’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye. 14 Zai karɓi gonakinku mafi kyau da gonakin inabinku da gonakin zaitunku yă ba wa ma’aikatansa. 15 Zai kuma karɓi zakan hatsinku da na inabinku yă ba shugabannin fadarsa da sauran masu hidimarsa. 16 Zai ƙwace bayinku maza da mata, da shanunku, da jakunanku mafi kyau domin su yi masa aiki. 17 Zai karɓi zakan dabbobinku, ku kanku za ku zama bayinsa. 18 Sa’ad da ranar ta zo, za ku yi kuka ku nemi a fishe ku daga sarkin da kuka zaɓa, Ubangiji kuwa ba zai ji ku ba.”
19 Amma mutanen suka ƙi jin Sama’ila, sai suka ce, “A’a, mu dai, muna son sarki yă bi da mu.” 20 Ta haka za mu zama kamar sauran ƙasashe, mu kasance da sarkin da zai bi da mu, yă tafi tare da mu zuwa yaƙe-yaƙe.
21 Da Sama’ila ya ji duk maganganun da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji. 22  Ubangiji kuwa ya ce, “Ka saurare su, ka naɗa masu sarki.”
Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa yă koma garinsa.”