22
Waƙar yabo da Dawuda ya yi
(Zabura 18.2-50)
1 Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu.
2 Ya ce,
“Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;
3 Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya
shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona.
Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona.
Daga mutane masu fitina, ka cece ni.
4 “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,
na kuwa tsira daga abokan gābana.
5 Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni;
raƙumar ruwan hallaka suna cin ƙarfina.
6 Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni;
tarkuna kuma suka auka mini.
7 “A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;
na yi kira ga Allahna.
Daga cikin haikalinsa ya saurare muryata;
kukata ta zo kunnensa.
8 Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza,
harsashan sararin sama sun jijjigu;
suka yi makyarkyata saboda yana fushi.
9 Hayaƙi ya taso daga kafaffen hancinsa;
harshen wuta mai cinyewa daga bakinsa,
garwashi mai ƙuna daga bakinsa.
10 Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa,
girgije mai duhu suna ƙarƙashin ƙafafunsa.
11 Ya hau kerubobi, ya tashi sama;
ya yi firiya a fikafikan iska.
12 Ya mai da duhu abin rufuwarsa
gizagizai masu kauri cike da ruwa suka kewaye shi.
13 Daga cikin hasken gabansa
garwashi wuta mai ci ya yi walƙiya.
14 Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama;
aka ji muryar Mafi Ɗaukaka.
15 Ya harbe kibiyoyi, ya wartsar da abokan gāba,
da walƙiya kuma ya sa suka gudu.
16 Aka bayyana kwarin teku,
tushen duniya suka tonu.
A tsawatawar Ubangiji,
da numfashinsa mai ƙarfi daga hancinsa.
17 “Daga sama ya miƙo hannu ya ɗauke ni,
ya tsamo ni daga zurfafa ruwaye.
18 Ya kuɓutar da ni daga hannun abokin gāba mai iko,
daga maƙiyina da suka fi ƙarfina.
19 Suka auka mini cikin ranar masifata,
amma Ubangiji ya kiyaye ni.
20 Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi;
ya kuɓutar da ni gama yana jin daɗina.
21 “Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina;
bisa ga tsabtar hannuwana ya sāka mini.
22 Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji;
ban yi wani mugun abu da zai juyar da ni daga Allahna ba.
23 Dukan dokokinsa suna a gabana;
ban ƙi ko ɗaya daga umarnansa ba.
24 Ba ni da laifi a gabansa
na kiyaye kaina daga yin zunubi.
25 Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina
bisa ga tsarkina a gabansa.
26 “Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci,
ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi,
27 ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki.
Amma ga masu karkataccen hali, kakan nuna kanka mai wayo.
28 Kakan ceci mai tawali’u,
amma idanunka suna a kan masu girman kai don ka ƙasƙantar da su.
29 Ya Ubangiji kai ne fitilata;
Ubangiji ya mai da duhuna haske.
30 Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji;
tare da Allahna zan iya hawan katanga.
31 “Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce;
maganar Ubangiji babu kuskure.
Shi garkuwa ce
ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi.
32 Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba?
Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?
33 Allah ne ya ba ni ƙarfi,
ya kuma mai da hanyata cikakkiya.
34 Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa;
ya sa na iya tsayawa a kan duwatsu.
35 Ya hori hannuwana don yaƙi,
hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.
36 Ka ba ni garkuwar nasararka;
ka sauko don ka sa in sami girma.
37 Ka fadada hanya a ƙarƙashina
domin kada idon ƙafana yă juya.
38 “Na fafari abokan gābana, na murƙushe su;
ban kuwa juya ba sai da na hallaka su.
39 Na hallaka su ƙaƙaf, ba kuwa za su ƙara tashi ba,
sun fāɗi a ƙarƙashin sawuna.
40 Ka ba ni ƙarfi don yaƙi;
ka sa maƙiyina suka rusuna a ƙafafuna.
41 Ka sa abokan gābana suka juya a guje,
na kuwa hallaka maƙiyina.
42 Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su,
suka yi kira ga Ubangiji, amma ba a amsa musu ba.
43 Na murƙushe su, suka yi laushi kamar ƙura;
na daka na kuma tattake su kamar caɓi a kan tituna.
44 “Ka kuɓutar da ni daga harin mutanena;
ka kiyaye ni kamar shugaban al’ummai.
Mutanen da ban sansu ba za su kasance a ƙarƙashina,
45 baƙi kuma su na zuwa don su yi mini fadanci;
da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya.
46 Zukatansu ta karaya;
suka fito da rawan jiki daga kagararsu.
47 “Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena!
Ɗaukaka ga Allah, Dutse, Mai Cetona!
48 Shi ne Allahn da yake rama mini,
wanda ya sa al’ummai a ƙarƙashina,
49 wanda ya kuɓutar da ni daga maƙiyina.
Ka ɗaukaka ni bisa maƙiyina;
ka kiyaye ni daga hannun mugayen mutane.
50 Saboda haka, zan yabe ka, ya Ubangiji cikin dukan al’ummai;
Zan rera waƙoƙin yabo ga sunanka.
51 “Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara;
ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa,
ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”