10
1 An yi wani Mutum a birnin Kaisariya, mai suna Karniliyas, shugaban sojoji ne na kungiyar da ake kira Italiya.
2 Mutum ne mai ibada, wanda ya mika kansa da iyalinsa ga bautar Allah; ya kan bada taimakon kudi mai yawa ga Yahudawa, kuma yana addu'a ko yaushe ga Allah.
3 Wajen sa'a ta tara ga yini, an bayyana masa cikin wahayi mala'kan Ubangiji na zuwa gare shi sai mala'ikan ya ce masa, ''Karniliyas!''
4 Karniliyas ya zuba wa mala'ikan ido a tsorace ya ce ''Menene, mai gida?'' mala'ikan ya ce masa, ''Addu'ar ka da taimakon ka ga talakawa ya kai sama matsayin sadaka abin tunawa a gaban Allah,
5 ''Yanzu ka aika mutane zuwa birnin Yafa su kawo mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus.
6 Yana zama tare da Saminu majemi, wanda gidansa ke bakin teku.
7 Da mala'ikan da ya yi magana da shi ya tafi, Karniliyas ya kira biyu daga barorin gidansa, da kuma soja guda mai bautar Allah daga cikin sojojin da suke masa hidima.
8 Karniliyas ya fada masu dukan abin ya faru sai ya aike su Yafa.
9 Washe gari wajen sa'a ta shida (tsakar rana) suna cikin tafiya da suka yi kusa da birni, Bitrus ya hau kan bene don ya yi addu'a.
10 Sai ya ji yunwa kuma yana bukatar wani abinda da zai ci, amma a yayin da mutanen na dafa abinci, sai ya ga wahayi.
11 Sai ya ga sararin sama ya bude kuma wani tasa na saukowa, wani abu kamar babban mayafi yana saukowa zuwa duniya, ana zuro shi ta kusuryoyinsa hudu.
12 A cikinsu kuwa akwai dukan halitun dabbobi masu kafa hudu da kuma masu rarrafe a duniya da tsunstayen sama.
13 Sai murya ta yi magana da shi; “Tashi, Bitrus, yanka ka ci ''
14 Amma Bitrus ya ce ''Ba haka ba, Ubangiji, gama ban taba cin abu mara tsarki ko mai kazanta ba.”
15 Amma muryar ta sake zuwa masa karo na biyu kuma; “Abinda Allah ya tsarkake, kada ka kira shi kazantacce.”
16 Wannan ya faru sau uku; nan da nan sai aka dauki tasar zuwa sama.
17 A yayin da Bitrus na cikin rudani game da ma'anar wahayin da ya gani, sai ga mutanen da Karniliyas ya aika suna tsaye a bakin kofar gidan, bayan sun tambayi hanyar zuwa gidan,
18 Kuma suka yi sallama suna tambaya ko Saminu wanda ake kira Bitrus ya sauka a nan.
19 A yayin da Bitrus yana kan tunani akan wahayin, Ruhu ya ce masa, “Duba, mutane uku na neman ka.”
20 Tashi ka sauka ka tafi tare da su. Kada ka yi jinkirin tafiya tare da su, domin Nine na aike su.”
21 Bitrus kuwa ya sauko wurin mutanen ya ce, “Ni ne wanda kuke nema. Me ya sa kuka zo?”
22 Suka ce, “Shugaban soja mai suna Karniliyas, adalin mutum kuma mai bautar Allah, yana da kyakkyawar shaida a dukan al'umman Yahudawa, shi ne wanda mala'ika mai tsarki na Allah ya aika domin ka zo gidansa, ya ji sako daga wurinka.”
23 Sai Bitrus ya gayyace su su zo ciki kuma su zauna tare da shi. Washegari sai ya tafi tare da su, kuma wadansu 'yan'uwa daga Yafa suka raka shi.
24 Kashegari suka shiga Kaisariya, Karniliyas kuwa yana jiran su; har ma ya gayyaci 'yan'uwansa da kuma abokansa na kusa.
25 Ya kasance sa'adda Bitrus ya shiga, Karniliyas ya sadu da shi kuma ya durkusa ya yi masa sujada.
26 Amma Bitrus ya tashe shi yana cewa, “Tashi tsaye! Ni ma mutum ne.”
27 A lokacin da Bitrus yake magana da shi, ya shiga ciki sai ya tarar da mutane da yawa sun taru a wuri daya.
28 Ya ce masu, “Ku da kanku kun sani bai dace Bayahuden mutum ya yi ma'amulla ko ya ziyarci wani ko wata kabila ba. Amma Allah ya ce da ni kada in ce da kowa mara tsarki ko kazantacce.
29 Wannan shine yasa na zo ba tare da musu ba, a lokacin da kuka kira ni. Don haka na tambaye ku me ya sa kuka aika in zo.”
30 Karniliyas ya ce “Kwanaki hudu da sun wuce a daidai wannan lokaci, ina addu'a da cikin sa'a na tara (karfe uku) a gidana, sai na ga mutum tsaye a gabana da tufafi mai haske.
31 Ya ce, “Karniliyas, Allah ya ji addu'ar ka, kuma taimakon ka ga talakawa ya tuna ma Allah da kai.
32 Saboda haka ka aika da wani Yafa, ya kira maka mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. Yana zama a gidan Saminu majemi, da ke bakin teku.
33 [Idan ya zo, zai yi magana da kai.]
34 Sai Bitrus ya bude bakinsa ya ce, “Gaskiya, na fahimci Allah baya nuna bambanci.
35 Maimakon haka, cikin kowace al'umma duk mai ibada kuma mai aikata adalci karbabbe ne a gare shi.
36 Ku kun san sakon da ya aika wa mutanen Isra'ila, a lokacin da ya sanar da labarin mai kyau na salama ta wurin Yesu Kristi, wanda shine Ubangiji na duka.
37 Ku da kanku kun san al'amuran da suka kasance, wanda ya faru cikin Yahudiya, farawa daga Galili, bayan sanarwar baftismar da Yahaya ya yi.
38 Al'amura game da Yesu Banazare, yadda Allah ya kebe shi da Ruhu Mai Tsarki da iko kuma. Ya kuma ci gaba da aikin alheri da warkarwa ga dukan wadanda shaidan ya daure, domin Allah yana tare da shi.
39 Mu shaidu ne ga dukan abubuwan da ya yi a kasar Yahudawa da cikn Urushalima, wannan Yesu wanda suka kashe, ta wurin giciye shi a akan itace.
40 Wannan mutumin, Allah ya ta da shi rana ta uku ya kuma maishe shi sananne,
41 ba ga dukan mutane ba, amma ga shaidun da Allah ya zaba tun da farko - mu kanmu, wadanda muka ci muka sha tare da shi bayan tashin sa daga matattu,
42 Ya umarce mu mu yi wa mutane wa'azi mu kuma tabbatar cewa shine wanda Allah ya zaba ya yi shariya bisa masu rai da matattu.
43 Gareshi ne dukan annabawa suka yi shaida, domin dukan wanda ya bada gaskiya gareshi ya sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.`
44 Sa'adda Bitrus yana kan magana game da wadannan abubuwa, Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan dukan wadanda suke sauraron wa'azin sa.
45 Mutanen da ke kungiyar masu bi da suka yarda da kaciya, dukan wadanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki, domin baiwar Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan al'ummai.
46 Domin sun ji al'umman nan suna magana da wasu harsuna suna yabon Allah. Sai Bitrus ya amsa,
47 “Ko akwai wanda zai hana wa wadannan baftisma ta ruwa, da shike suma sun karbi Ruhu Mai Tsarki kamar mu?”
48 Sai ya ba da umarni a yi masu baftisma cikin sunan Yesu Kristi. Sai suka roke shi ya kasance da su na wasu kwanaki.