2
Da ranar Fentikos ta zo, dukansu suna tare wuri daya. Nan da nan sai ga wata kara daga sama kamar ta babbar iska, kuma ta sauko ta cika duka gidan inda suke zaune. Sai ga wasu harsuna kamar na wuta sun bayyana a garesu aka rarraba su, kuma suka zauna bisa kowannensu. Dukansu suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka fara magana da wadansu harsuna, yadda Ruhu ya ba su iko su yi magana. A lokacin akwai Yahudawa dake zaune a Urushalima, mutanen Allah, daga kowace kasa karkashin sama. Da suka ji wannan kara jama'a duk suka taru suka rude saboda kowannensu ya ji suna magana da harshensa. Suka yi mamaki matuka; suka ce, ''Lallai, wadannan duka ba Galiliyawa ba ne? Yaya mu ke jinsu duka, kowannensu na magana a cikin harshen da aka haife mu? Fisiyawa da Mediyawa da Elimawa, da Yahudawa da Kafadokiya, cikin Fontus da Asiya, 10 cikin Firgia da Bamfiliya, cikin Masar da yankunan Libiya ta wajen Sur, da baki daga Roma, 11 Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah.'' 12 Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, ''Menene ma'anar wannan?'' 13 Amma wasu suka yi ba'a suka ce, ''Sun bugu ne da sabon ruwan inabi.'' 14 Amma Bitrus ya tashi tare da sha dayan, ya daga murya ya ce da su, ''Mutanen Yahuda da dukanku dake zaune a Urushalima, bari ku san wannan; ku saurari maganata. 15 Domin wadannan mutanen ba buguwa suka yi ba yadda kuke zato, domin yanzu karfe tara ne na safe kawai. 16 Amma wannan shine abinda aka fada ta wurin annabi Yowel. 17 Allah ya ce, 'Haka zai kasance a kwanakin karshe, zan zubo Ruhuna a kan dukan mutane, 'ya'yanku maza da mata za su yi anabci, kuma samarinku za su ga wahayoyi, kuma tsofaffinku za su yi mafarkai. 18 Haka kuma a bisa bayi na maza da mata, a kwanakin nan zan zubo da Ruhuna, kuma za su yi anabci. 19 Zan nuna al'ajibai a sararin sama da kuma alamu a bisa duniya, jini da wuta, da girgije. 20 Rana zata juya ta koma duhu kuma wata ya koma jini, kafin Babbar ranan nan ta Ubangiji ta zo. 21 Zai kuma zama dukan wanda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto. 22 Mutanen Isra'ila, ku saurari wadannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar da shi gareku ta wurin manyan ayyuka da ban mamaki da alamu da Allah ya yi ta wurinsa a tsakiyarku, kamar yadda ku da kanku kuka sani. 23 Saboda tabbataccen shiri da riga sani na Allah, aka bayar dashi, ku kuma, ta hannun mutane 'yan tawaye, kuka gicciye shi kuma kuka kashe shi. 24 Wanda Allah ya tayar, bayan ya cire zafin mutuwa daga gareshi, saboda ba zai yiwu ba ta rike shi. 25 Gama, game da shi, 'Ina ganin Ubangiji a gabana ko yaushe, domin yana gefen hannun damana saboda kada in firgita. 26 Saboda haka zuciyata na farin ciki harshena yana yin murna. Kuma, jikina zai zauna gabagadi. 27 Gama ba za ka watsar da raina a lahira ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka ya ga ruba ba. 28 Ka bayyana mani hanyar rai; da fuskarka zaka cika ni da farin ciki. 29 'Yan'uwa, zan yi magana da ku gabagadi game da baba Dauda: ya mutu kuma aka bizne shi, kuma kabarinsa na nan tare da mu har yau. 30 Domin haka, don shi annabi ne kuma ya san Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa daga cikin zuriyarsa zai sanya wani bisa kursiyinsa. 31 Ya hango wannan al'amari kuma ya yi magana game da tashin Almasihu, 'Ba ayi watsi da shi ba a lahira, kuma jikinsa bai ga rubewa ba.' 32 Wannan Yesun - Allah ya tashe shi, wanda dukanmu shaidu ne. 33 Saboda haka yadda aka tashe shi zuwa hannun dama na Allah kuma ya karbi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, shine ya zubo mana wannan da kuke gani kuma kuke ji. 34 Dauda bai hau zuwa sama ba, amma ya ce, ''Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna hannun dama na, 35 har sai na maida makiyanka abin takawar sawunka.''' 36 Saboda haka, bari gidan Isra'ila su sani tabbas wannan Yesun wanda kuka gicciye, Allah ya maishe shi Ubangiji da kuma Almasihu. 37 Da suka ji haka sai suka soku a zukatansu, suka cewa Bitrus da sauran manzanni, '''Yan'uwa me za mu yi?'' 38 Sai Bitrus ya ce masu, ''Ku tuba ayi wa kowannenku baftisma, cikin sunan Yesu Almasihu domin gafarar zunubanku, kuma za ku karbi baiwar Ruhu Mai Tsarki. 39 Domin alkawarin a gareku ne da 'ya'yanku da duk wadanda ke nesa, dukan iyakar mutanen da Ubangiji Allahnmu zai kira.'' 40 Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, ''Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara.'' 41 Sai suka karbi maganar sa kuma aka yi ma su baftisma, a wannan rana kuma aka sami karin rayuka wajen dubu uku. 42 Su ka cigaba cikin koyarwar manzanni da zumunta, cikin kakkaryawar gurasa da kuma cikin addu'o'i. 43 Tsoro ya sauko bisa kowane rai, kuma aka yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin. 44 Duka wadanda suka ba da gaskiya suna tare kuma komai nasu na kowanensu ne, 45 kuma suka saida kadarorinsu da mallakarsu kuma suka rarrabawa kowa, bisa ga irin bukatar da kowannensu yake da ita. 46 A kowace rana suka cigaba tare da nufi daya a cikin haikali, suna kakkarya gurasa a gidaje, kuma suna raba abinci tsakaninsu cikin farin ciki da tawali'u a zuciya; 47 Suna yabon Allah kuma suna da tagomashi a gaban dukan mutane. Ubangiji kuma kullum yana kara masu wadanda suke samun ceto.