28
Sa'adda muka sauka lafiya, sai muka ji cewa sunan tsibirin Malita. Mutanen garin sun nuna mana alheri matuka don sun hura wuta don mu ji dimi, saboda ruwan sama da sanyin da ake yi. Amma sa'adda Bulus ya tara kiraruwa don hura wuta, sai maciji saboda zafin wuta, ya fito ya nade hannuwansa. Da mazaunan garin suka ga maciji ya nade hannuwansa, sai suka cema junansu, “Ba shakka wannan mutumin mai kisan kai ne, koda shike ya tsira daga Teku, sharia baza ta barshi da rai ba”. Amma ya karkade macijin cikin wuta ba tare da ya cutar da shi ba. Sun saurara su gani ko zai kumbura ko ya fadi matacce. Amma da suka jira dan lokaci basu ga wata matsala ta same shi ba sai suka canza tunaninsu sukace shi wani allah ne. A kusa da wannan wurin tsibirin akwai wasu gonakin wani babban mutumin tsibirin, mai suna Babiliyas. Ya karbe mu ya biya bukatun mu har kwana uku. Ana nan ashe mahaifin Babiliyas yana fama da zazzabi da atuni. Bulus ya shiga, yayi masa addu'a, ya dibiya masa hannu, ya sami warkarwa. Sa'adda wannan ya faru, sauran marasa lafiya da ke tsibirin sun zo sun sami warkarwa. 10 Mutanen sun mutunta mu kwarai. Yayin da muke shirin tafiya, sun bamu duk abinda muke bukata. 11 Bayan watanni uku, mun shiga jirgin Iskandariya wanda tun da hunturu yake a tsibirin mai zane kamannin Tagwaye Maza. 12 Bayan saukar mu a birnin Sirakus, mun yi kwana uku a wurin. 13 Daga nan sai muka tafi, har muka zo birnin Rigiyum. Bayan kwana daya iska mai karfi daga kudu ta taso, a cikin kwana biyu muka iso Butiyoli. 14 A can muka iske wasu 'yan'uwa suka roke mu mu zauna tare da su har kwana bakwai. Ta wannan hanyar ce muka zo Roma. 15 Daga can da 'yan'uwa suka ji labarin mu, suka fito don su tarbe mu tun daga Kasuwar Abiyas da kuma Rumfuna Uku. Da Bulus ya gan su, ya yi wa Allah godiya ya kuma sami karfafawa. 16 Sa'adda muka shiga Roma, aka yardar wa Bulus ya zauna shi kadai tare da sojan da ke tsaronsa. 17 Ana nan bayan kwana uku, Bulus ya kira shugabannin Yahudawa. Bayan da suka taru, sai ya ce masu, “Yan'uwa, ko da shike ban yi wa kowa laifi ko keta al'adun Ubanninmu ba, duk da haka an bashe ni daurarre tun daga Urushalima zuwa ga hannunwan mutanen Roma. 18 Bayan tuhumata, sun yi kudirin saki na, domin ban yi laifin da ya cancanci mutuwa ba. 19 Amma da Yahudawa suka tsaya a kan ra'ayin su, ya zama dole in daukaka kara zuwa ga Kaisar, ba domin ina da wani dalilin da zan yi karar al'ummata ba ne. 20 Saboda wannan ne na bukaci ganinku in yi magana da ku. Saboda begen da Isra'ila suke da shi ya sa nake daure da wannan sarkar”. 21 Sai suka ce masa, “Bamu karbi wasiku daga Yahudiya game da kai ba, babu kuma wani daga cikin 'yan'uwa wanda ya kawo mana wani rahoto ko wata magana game da kai. 22 Amma muna so mu ji daga gare ka abin da kayi tunani ka kuma gani game da wannan darikar, gama mun sani ana kushenta a ko'ina.” 23 Sa'adda suka sa masa rana, mutane da dama suka same shi a masaukinsa. Ya gabatarda zantattukan a gare su, yana tabbatar da bayyanuwar mulkin Allah. Har ya nemi ya rinjaye su a kan zancen Yesu, tun daga attaurat ta Musa zuwa litattafan annabawa, ya yi wannan tun daga safiya har yamma. 24 Wasu sun kawar da shakkar abin da aka fada, amma wadansu basu gaskanta ba. 25 Da shike ba su yarda da junansu ba, sai suka tafi bayan da Bulus ya fadi kalma daya, “Ruhu Mai Tsarki ya yi magana ta bakin annabi Ishaya zuwa ga kakanninku. 26 Ya ce, 'Jeka wurin al'umman nan ka ce, cikin ji zaku ji amma ba zaku fahimta ba; zaku gani amma ba zaku gane ba. 27 Amma zuciyar mutanen nan ta yi kanta, kunnuwansu sun ji da kyar, sun rufe idanunsu; don kada su gani su gane, su kuma ji da kunuwansu, kuma su fahimta da zuciyarsu, domin su juyo ni kuma in warkar da su.” 28 Saboda haka, sai ku sani cewa wannan ceto na Allah an aikar da shi zuwa ga Al'ummai, za su kuma saurara.” 29 [Sa'adda ya fadi wannan zantattuka, Yahudawa suka tashi, suna gardama da junansu.] 30 Bulus ya zauna shekaru biyu a cikin gidan hayarsa, yana marabtar duk wadanda suka zo wurinsa. 31 Yana wa'azin mulkin Allah, yana koyarwa da al'amuran Ubangiji Yesu Kristi gaba gadi. Ba wanda ya hana shi.