8
1 Bulus ya amince da mutuwarsa. A wannan rana tsanani mai zafi ya fara tasowa akan Iklisiya da take a Urushalima, sai masu bangaskiya duka suka bazu ko ina a cikin garuruwan Yahudiya da Samariya, sai manzannin kadai aka bari.
2 Amintattun mutane suka bizne Istifanus suka yi babban makoki game da shi.
3 Amma Shawulu ya yi wa Iklisiya mugunta kwarai, ya dinga shiga gida gida yana jawo mutane maza da mata, kuma yana kulle su cikin kurkuku.
4 Duk da haka masu bangaskiyar nan da suka warwatsu suka tafi suka dinga yada wa'azin maganar.
5 Filibus ya tafi can Samariya ya yi shelar Almasihu.
6 Da taron mutane suka ji kuma suka ga alamun da Filibus yake yi, sai suka mai da hankali dukansu domin su ji abinda yake fadi.
7 Domin kazaman ruhohi sun fito daga cikin mutane da yawa da suka saurare shi suna kuka da kururuwa; nakasassun mutane dayawa da guragu suka warke.
8 Kuma aka yi farin ciki mai girma a birnin.
9 Amma akwai wani mutum a cikin birnin da ake kira Siman, wanda tun farko shi masafi ne da kuma dan dabo, yana yi wa mutanen Samariya abubuwan ban mamaki, yayin da yake kiran kansa wani mai muhimmanci.
10 Dukan Samariyawa, manya da yara, suna sauraronsa, su kan ce, ''Wannan mutum shine ikon Allahn nan wanda ake kira mai girma.''
11 Suna sauraron sa, domin ya dade yana yi masu abubuwan mamaki da tsafe-tsafensa.
12 Amma da suka yi bangaskiya da wa'azin bisharar da Filibus yake yi game da mulkin Allah da sunan Yesu Almasihu, sai aka yi masu Baftisma dukansu maza da mata.
13 Har shima Siman da kansa ya ba da gaskiya. Bayan an yi masa Baftisma ya cigaba da bin Filibus, da ya ga ana nuna alamu da manyan ayyuka, sai ya yi mamaki.
14 Da manzannin da ke Urushalima suka ji labarin Samariya ta karbi maganar Allah, sai suka aika masu Bitrus da Yahaya.
15 Da suka iso, suka yi masu addu'a, domin su karbi Ruhu Mai Tsarki.
16 Domin har wannan lokaci, Ruhu Mai Tsarki bai sauko kan kowannensu ba; an dai yi masu baftisma ne kadai cikin sunan Ubangiji Yesu.
17 Sai Bitrus da Yahaya suka dora masu hannuwansu, sai suka karbi Ruhu Mai Tsarki.
18 Sa'adda Siman yaga ana bayar da Ruhu Mai Tsarki ta wurin dorawar hannuwan manzanni, ya basu kudi.
19 Ya ce, “Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki.''
20 Amma Bitrus yace masa, ''Azurfarka ta lalace tare da kai, saboda kana tunanin za ka malaki baiwar Ubangiji da kudi.
21 Baka da wani rabo a wannan al'amari, domin zuciyarka ba daidai take da Allah ba.
22 Saboda haka ka tuba daga wannan muguntarka, ka kuma yi addu'a ga Ubangiji, domin mai yiwuwa ya gafarta maka game da manufar zuciyarka.
23 Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi.''
24 Siman ya amsa ya ce, ''Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni.''
25 Sa'anda Bitrus da Yahaya suka bada shaida kuma suka fadi maganar Ubangiji, sun koma Urushalima; akan hanya, suka yi wa'azin bishara a kauyukan samariyawa da yawa.
26 Yanzu kuwa Mala'ikan Ubangiji ya yi wa Filibus magana cewa, ''Tashi ka tafi ta kudu da hanyar da ta yi kasa daga Urushalima zuwa Gaza'' (wannan hanyar yana cikin hamada.)
27 Ya kuwa tashi ya tafi. Sai ga wani mutum daga Habasha, baba ne mai babban matsayi a karkashin Kandakatu, sarauniyar Habasha. Shine yake mulkin dukan dukiyarta. Ya zo Urushalima domin ya yi ibada.
28 Yana komawa zaune cikin karussarsa, kuma yana karanta Littafin annabi Ishaya.
29 Ruhun ya ce wa Filibus, ''Ka je kusa da karussar nan.''
30 Sai Filibus ya gudu ya same shi, kuma ya ji shi yana karanta littafin annabi Ishaya, sai ya ce, ''Ka fahimci abin da kake karantawa?''
31 Bahabashen ya ce. ''Yaya zan iya, idan ba wani ya bishe ni ba?'' Ya roki Filibus ya shigo cikin karussar ya zauna tare da shi.
32 Wannan kuwa shine nassin da Bahabashen yake karantawa, ''An kai shi kamar tunkiya zuwa mayanka; shiru kuma, kamar dan rago a hannun masu sosayarsa, bai bude baki ba.
33 Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci: Wa zai bada tarihin tsararsa? Domin an dauke ransa daga duniya.''
34 Sai baban ya tambayi Filibus, ya ce, ''Na roke ka, gaya mani, game da wa annabin yake magana? Da kansa, ko kuwa wani mutum dabam?''
35 Filibus ya fara magana; akan littafin Ishaya, ya kuwa yi masa wa'azi akan Yesu.
36 Yayin da suke tafiya akan hanya, sai suka iso bakin wani kogi; Baban ya ce, “Duba, ga ruwa anan; me zai hana ayi mani baftisma?”
37 Filibus ya ce,” Idan ka gaskanta da zuciya daya, ana iya yi maka baftisma.” Sai Bahabashen ya ce, “Na gaskata Yesu Almasihu shine Dan Allah.”
38 Sai Bahabashen ya umarta a tsai da karussar. Sai suka zo wurin ruwa dukan su biyu, Filibus da baban, Filibus kuwa yayi masa baftisma.
39 Yayin da suka fito daga cikin ruwan, Ruhun Ubangiji ya dauke Filibus; baban bai sake ganin shi ba, sai ya ci gaba da tafiyar sa yana murna.
40 Amma Filibus ya bayyana a Azotus. Ya ratsa wannan yankin yana wa'azin bishara a dukan garuruwan, har sa'anda ya iso Kaisariya.