12
Game da baye bayen Ruhu Mai Tsarki 'yan'uwa, bana so ku zama da jahilci. Kun san cewa lokacin da ku ke al'ummai, an rude ku da alloli marasa magana ta hanyoyi dabam dabam marasa kan gado. Saboda haka ina so ku sani babu wanda ya ke magana da Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la'ananne ne.” Babu kuma wanda zaya ce, “Yesu Ubangili ne,” sai dai ta Ruhu Mai Tsarki. Akwai bay bye iri iri, amma Ruhu daya ne. Akwai hidimomi iri iri, amma Ubangiji daya ne. Akwai aikace aikace iri iri, amma Allah daya ke bayyanawa kowane mutum yadda zai aiwatar da su. To ga kowanne an bayar da ikon nuna ayyukan Ruhu a fili domin amfanin kowa. Ga wani ta wurin Ruhu an bayar da baiwar hikima, kuma ga wani kalmar sani ta wurin Ruhu daya. Ga wani an ba shi baiwar bangaskiya ta wurin Ruhun nan, ga wani kuwa an ba shi baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhun. 10 Ga wani yin ayyukan iko, ga wani kuwa annabci. Ga wani kuwa an ba shi baiwar bambance ruhohi, ga wani harsuna daban daban, kuma ga wani fassarar harsuna. 11 Dukan wadannan Ruhu daya ne ya ke iza su, ya kuma rarraba baye bayen ga kowannen su yadda ya nufa. 12 Kamar yadda jiki daya ne amma da gabobi da yawa kuma duk gabobin na jiki daya ne, haka nan Almasihu yake. 13 Gama ta Ruhu daya aka yi wa kowa baftisma cikin jiki daya, ko Yahudawa ko al'ummai, ko bayi ko 'ya'ya, dukan mu kuwa an shayar da mu Ruhu daya. 14 Gama jiki ba daya ba ne sungun, amma gabobi ne da yawa. 15 Idan kafa ta ce, “tun da dai ni ba hannu ba ne to ni ba fannin jikin bane,” wannan baya rage masa matsayin sa a jikin ba. 16 Kuma da kunne zaya ce, '''Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gabar jiki ba ne,'' fadar haka ba za ta raba shi da zama gabar jikin ba. 17 Idan dukan jikin ya kasance ido ne da me za a ji? Da dukan jikin kunne ne, da me za a sunsuna? 18 Amma Allah ya shirya gabobin jiki bisa ga tsarin sa. 19 Amma da duk jiki gaba daya ce, da ina jikin zai kasance? 20 Ga shi akwai gabobi da yawa, kuma jiki daya ne. 21 Ba da ma ido ya fadawa hannu, ''Bana bukatar ka,'' ko kuma kai ya fadawa kafafu, ''Ba na bukatar ku.'' 22 Amma, sai ma gabobin da ake gani kamar raunannu su ne masu humimmanci, gabobin jiki kuwa da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mu kan fi ba su martaba. 23 Ta haka gabobinmu marasa kyan gani, akan kara kyautata ganinsu. Gabobin mu masu kyan kuma ba sai an yi masu ado ba. 24 Amma Allah ne da kansa ya hada jiki, yana bada mafificiyar martaba ga kaskantacciyar gaba. 25 Yayi haka ne domin kada a sami tsattsaguwa a cikn jikin, amma domin gabobin su kula da juna da matsananciyar lura. 26 Kuma idan gaba daya na wahala, dukan gabobin suna wahala tare. ko kuma idan an girmama gaba daya, dukan gabobin na farin ciki tare. 27 Yanzu ku jikin Almasihu ne, saboda haka kuma kowannen ku gabarsa ne. 28 A cikin ikilisiya, Allah ya sa wasu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin ayyukan iko, sai masu aikin warkarwa, da masu bayar da taimako, da masu aikin tafiyar da al'amura, da masu harsuna daban daban. 29 To kowa manzo ne? ko kuwa duka annabawa ne? ko kuma duka masu koyarwa ne? Kowa ne ke yin manyan ayyukan iko? 30 Ko kuwa dukan su ne suke da baiwar warkarwa? Dukan su ne ke magana da harsuna? ko kuma dukan su ne ke fassara harsuna? 31 Amma bari ku himmantu ga neman baiwa mafi girma. Kuma zan nuna maku wata hanya mafificiya.