11
1 Ina fatan za ku jure da ni cikin wauta kadan. Ko da yake lallai kuna jurewa da ni!
2 Domin ina kishi sabili da ku. Kishi na kuwa irin na Allah ne domin ku. Tun da na alkawartar da ku a cikin aure ga miji daya. Na kuma yi alkawarin in gabatar da ku kamar budurwa mai tsarki ga Almasihu.
3 Gama ina fargaba a kan ku, ko watakila, kamar yadda macijin ya yaudari Hauwa'u ta wurin kissarsa, Ya zamana tunaninku ya kauce daga sahihiyar sadaukarwa ga Almasihu.
4 Anar misali idan wani ya zo ya kawo shelar wani Yesu daban da wanda muka yi maku wa'azinsa. Ko kuma kun karbi wani ruhu daban da wanda muka karba. Ko kuma kun karbi wata bishara daban da wadda muka karba. Amincewar da kuka yi wa wadannan abubuwa ta isa!
5 Don kuwa ina tsammanin ba a baya nake ba ga sauran wadanda ake kira manyan manzanni.
6 To ko ma ba a ilimantar da ni ba akan yin jawabi, ban rasa horarwar ilimi ba. Ta kowace hanya kuma cikin abubuwa duka mun sanar da ku wannan.
7 Na yi zunubi ne da na kaskantar da kai na domin a daukaka ku? Domin na yi maku wa'azin bisharar Allah kyauta.
8 Na yi wa sauran Ikilisiyoyi kwace ta wurin karbar gudummuwa daga wurin su domin inyi maku hidima.
9 Lokacin da ina tare da ku kuma na sami kai na cikin bukata, ban dora wa kowa nauyi ba. Domin 'yan'uwa da suka zo daga Makidoniya sun biya bukatuna. A cikin komai na kebe kaina daga zama nawaya a gare ku, kuma zan cigaba da yin haka.
10 Kamar yadda gaskiyar Almasihu ke ciki na, ba zan yi shiru da wannan fahariya tawa ba a cikin dukan kasar Akaya.
11 Don me? Saboda ba na kaunar ku? Allah ya sani.
12 Amma abinda na ke yi, zan cigaba da yi. Zan yi haka ne domin in yanke zarafin wadanda ke son samun zarafi kamar mu akan abubuwan da suke fahariya da shi.
13 Don irin wadannan mutane manzannin karya ne masu aikin yaudara. Suna badda kama kamar manzannin Almasihu.
14 Wannan ba abin mamaki ba ne, domin shaidan ma yakan badda kama ya fito kamar mala'ikan haske.
15 Ba wani babban abin mamaki ba ne idan bayin sa sun badda kamanninsu don a dauka bayin adalci ne su. Karshen su zai zama sakamakon abin da suka aikata.
16 Ina kara fadi: Kada wani ya yi zaton ni wawa ne. Idan kun yi zaton hakan, to ku dauke ni kamar wawan don inyi fahariya kadan.
17 Abinda nake fadi game da wannan gabagadi mai fahariya ba bisa ga amincewar Ubangiji ba ne, amma ina magana a matsayin wawa.
18 Tun da mutane dayawa suna fahariya bisa ga jiki, ni ma zan yi fahariya.
19 Gama kuna murnar tarayya da wawaye. Ku masu hikima ne!
20 Kuma kuna hakuri da wanda zai bautar da ku, idan ya tauye ku, yana amfani da ku don ribar kansa, idan ya dauki kansa fiye da ku, ko ya mammare ku a fuska.
21 Ina mai cewa mun kunyata da muka rasa gabagadin yi maku haka. Duk da haka idan wani zai yi fahariya-Ina magana kamar wawa-Ni ma zan yi fahariya.
22 Su yahudawa ne? Ni ma haka. Su Isra'ilawa ne? Nima haka. Su zuriyar Ibrahim ne? Nima haka.
23 Su bayin Almasihu ne? (Ina magana kamar ba ni cikin hankalina) na fi su ma. Na ma yi aiki tukuru fiye da su duka, shiga kurkuku fiye da kowa, a shan duka babu misali, a fuskantar haduran mutuwa da yawa.
24 Daga hannun yahudawa sau biyar na sha bulala ''Arba'in ba daya''.
25 Sau uku na sha dibga da sanduna. Sau daya aka jejjefe ni da duwatsu. Sau uku na yi hadari a jirgin ruwa. Na yi tsawon dare da yini guda a tsakiyar teku.
26 Ina shan tafiye tafiye, cikin hadarin koguna, cikin hadarin 'yan fashi, cikin hadari daga mutane na, cikin hadari daga al'ummai, cikin hadarin birni, cikin hadarin jeji, cikin hadarin teku, cikin hadarin 'yan'uwan karya.
27 Na sami kaina ina aiki tukuru cikin mawuyacin hali, cikin yin dare dayawa ba barci, cikin yunwa da kishin ruwa, cikin yawan azumi, cikin sanyi da tsiraici.
28 Baya ga wadannan duka, akwai nauyi a kaina kullayaumin saboda damuwata akan Ikkilisiyoyi duka.
29 Waye kumama, wanda ban zama kumama akan shi ba? Wanene aka sa yayi tuntube, kuma ban kuna ba?
30 Idan zan yi fahariya, zan yi fahariya akan abinda ke nuna kasawata.
31 Allah kuma Uba na Ubangijinmu Yesu, wanda ya isa yabo har abada, ya san ba karya nake yi ba!
32 A Damasku, gwamnan da ke mulki karkashin sarki Aritas yasa aka yi tsaron birnin Damasku domin a kama ni.
33 Amma ta taga cikin kwando aka ziraro ni bayan ganuwar birni, na kuwa kucce daga hannunsa.