8
1 Muna so ku sani, 'yan'uwa, game da alherin Allah da aka bayar ga Ikkilisiyoyin Makidoniya.
2 A lokacin babban gwajin wahala, yalwar farincikinsu da tsananin talaucinsu ya haifar da yalwar bayarwa hannu sake.
3 Domin ina shaida, sun yi bayarwa iya kokarinsu, fiye da abinda ma suke iyawa. Cikin yaddar ransu
4 da roko mai yawa suka nace da a ba su zarafi su yi tarayya a wannan hidima ga masu bi.
5 Haka ya auku ba kamar yadda muka yi zato ba. A Maimakon haka, sai da suka fara bada kansu ga Ubangiji. Kuma suka bada kansu gare mu bisa ga nufin Allah.
6 Sai muka karfafa Titus, wanda ya rigaya ya fara wannan aiki, domin ya kammala wannan aiki na bayarwa ta fannin ku.
7 Amma kun habaka cikin komai-cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin aiki tukuru, cikin kaunarku dominmu. Don haka, ku tabbata kun habaka a wannan aiki na bayarwa.
8 Na fadi haka ne ba kamar ina umurtar ku ba. A maimakon haka, na fadi haka ne in gwada sahihancin kaunarku ta wurin kwatanta ta da himmar sauran mutane.
9 Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu. Kodashike shi mai arziki ne, amma ya zama matalauci, domin ta wurin talaucinsa ku yi arziki.
10 A wannan al'amari zan ba ku shawarar da za ta taimake ku. Shekarar da ta wuce, ba fara wani abu kawai kuka yi ba, amma kun yi marmarin ku yi shi.
11 Yanzu ku kammala shi. Kamar yadda kuke da niyya da marmarin yin haka a lokacin, bari ku yi kokari ku kawo shi ga kammalawa iyakar iyawar ku.
12 Idan kuna niyya ku yi wannan aiki, abu mai kyau ne karbabbe kuma. Tabbas ya zama dai-dai da abinda mutum ke da shi, ba abinda ba ya da shi ba.
13 Domin wannan aiki ba domin a nawaita maku sannan wadansu su samu sauki ba ne. A maimakon haka, ya kamata a sami daidaituwa.
14 Yalwar ku a wannan lokaci za ta zama abin biyan bukatarsu. Haka nan kuma domin yalwar su ta iya biyan bukatarku, domin a sami daidaituwa.
15 Yana nan kamar yadda aka rubuta: “Wanda ke da shi dayawa bai samu raguwar komai ba, kuma wanda yake da kadan bai rasa komai ba.”
16 Amma godiya ga Allah, da yasa a zuciyar Titus marmarin kulawa da ku kamar wadda nake da ita domin ku.
17 Gama ba rokon mu kadai ya karba ba, amma ya yi da gaske akan haka. Ya zo gare ku ne da yardar kan sa.
18 Mun aiko tare da shi dan'uwa da ake yaba masa a tsakanin dukan Ikkilisiyoyi domin ayyukansa a cikin shelar bishara.
19 Ba domin wannan kadai ba, amma Ikkilisiyoyi ne suka zabe shi ya tafi tare da mu a cikin yin wannan hidima ta alheri. Wannan domin girmama Ubangiji ne kansa da kuma domin aniyarmu ta taimakawa.
20 Muna gudun kada kowa ya sa mana laifi game da wannan alheri da muke dauke da shi.
21 Niyyar mu ce mu yi kyakkyawan abu, ba a gaban Ubangiji kadai ba, amma a gaban mutane ma.
22 Mun kuma aiki wani dan'uwan tare da su. Mun sha gwada shi, kuma mun same shi da himma wajen ayyuka da dama. Yanzu kuma ya kara himma, saboda amincewa mai girma da yake da ita gare ku.
23 Game da Titus, shi abokin tafiyata ne, kuma abokin aikina domin ku. Game da yan'uwanmu, an aiko su ne daga Ikkilisiyoyi. Su kuwa daraja ne ga Almasihu.
24 Don haka, ku nuna masu kaunarku, ku kuma nuna wa Ikilisiyoyi dalilin fahariyarmu game da ku.