6
1 'Ya'ya, ku yi biyayya ga iyayenku chikin Ubangiji, domin wannan daidai ne.
2 “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka” (Doka ta fari kenan da alkawari),
3 “ta haka za ku yi albarka, domin kwanakinku su yi tsawo a duniya”.
4 Hakanan, ku ubanni kada ku cakuni 'ya'yan ku har su yi fushi, amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargadinsa.
5 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya tare da girmamawa da tsoro da zuciya mai gaskiya. Ku yi masu biyayya kamar ga Almasihu.
6 Ku yi masu biyayya ba don lallai suna kallonku ba domin ku faranta masu rai. Maimakon haka, ku yi biyayya kamar bayi ga Almasihu. Ku yi nufin Allah daga zuciya.
7 Ku yi hidima da dukan zuciya, kamar kuna bautar Ubangiji ba mutane ba.
8 Sai ku sani cewa duk abinda mutum ya yi zai karbi sakamako daga wurin Ubangiji, ko shi bawa ne ko 'yantacce.
9 Ku kuma iyayengiji, ku yi irin wannan ga barorin ku. Kada ku razana su. Kun sani shi wanda ke Ubangijinsu da ku daya ne yana sama. Kun sani tare da shi baya nuna tara.
10 A karshe, ku karfafa cikin Ubangiji da cikin karfin ikonsa.
11 Ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa gaba da dabarun shaidan.
12 Gama yakinmu ba da nama da jini bane. Amma, da ikoki da mulkoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu duhu na mugunta cikin sammai.
13 Don haka ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya tsayawa da karfi cikin muguwar rana. Bayan kun yi komai za ku tsaya da karfi.
14 Saboda haka ku tsaya da karfi. Ku yi wannan bayan kun yi damara cikin gaskiya kuna yafa sulke na adalci.
15 Ku yi wannan bayan kun daure kafafunku da shirin kai bisharar salama.
16 Cikin dukan abu ku dauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku kashe dukan kibau masu wuta na mugun.
17 Ku dauki kwalkwalin ceto da takobin Ruhu, wanda shine maganar Allah.
18 Tare da kowacce irin addu'a da roko kuna addu'a kullum cikin Ruhu. Da wannan lamiri, kuna tsare wannan da iyakacin kula da dukan juriya da roko saboda dukan masu bi.
19 Ku yi mani addu'a, domin in karbi sako duk sa'adda na bude bakina. Ku yi addu'a in sami gabagadin bayyana boyayyar gaskiyar bishara.
20 Saboda bishara nake jakada cikin sarkoki, yadda a cikinta zan yi magana gabagadi yadda takamata.
21 Amma domin ku san rayuwa ta, da yadda nake, Tikikus, dan'uwa kaunatacce da amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai sanar da ku dukan abu.
22 Saboda wannan dalili na aiko shi gare ku, domin ku san al'amuran mu, kuma domin ku sami ta'aziya a zukatan ku.
23 Bari salama ta kasance tare da 'yan'uwa, kauna da bangaskiya daga wurin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu.
24 Alheri ya kasance tare da wadannan da suke kaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu tare da kauna mara mutuwa.