17
1 Da Yesu ya fadi wandannan abubuwa, sai ya tada idanunsa sama ya ce, ya Uba, sa'a ta zo; ka daukaka Danka, domin Dan shi ya daukaka ka,
2 kamar yadda ka ba shi iko akan dukkan 'yan adam, ya ba da rai madawwami ga duk wanda ka ba shi.
3 Wannan ne rai madawwami: wato su san ka, Allah makadaici na gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Almasihu.
4 Na daukaka ka a duniya, na gama aikin da ka ba ni in yi.
5 Yanzu, ya Uba, ka daukaka ni tare da kai da daukaka wadda ni ke da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasanci.
6 Na bayyana sunanka ga mutunen da ka ba ni acikin duniya. Na ka suke, ka ba ni su, sun kuwa kiyaye maganarka.
7 Yanzu kuwa sun san duk iyakar abinda ka ba ni daga gare ka yake,
8 don kuwa maganganun da ka fada mani. Na fada masu, sun kuma karba, sun sani kuwa hakika na fito daga gareka ne, kuma sun gaskata kai ne ka aiko ni.
9 Ina yi masu addu'a. Ba domin duniya ni ke yin addu'a ba, amma domin wadanda ka bani gama na ka ne.
10 Gama dukan abinda ke nawa na ka ne, naka kuwa nawa ne, an kuma daukaka ni a cikinsu.
11 Ba na cikin duniya kuma, amma wadannan mutane suna cikin duniya, ni kuwa ina zuwa wurin ka. Ya Uba mai Tsarki, ka adanasu cikin sunanka da ka ba ni domin su zama daya, kamar dai yadda muke daya.
12 Lokacin da ina tare da su, na adanasu acikin sunanka da ka ba ni. Na kiyaye su, kuma ko daya kuwa daga cikinsu ba ya bace ba, sai dai dan hallakar nan, domin Nassi ya cika.
13 Amma yanzu ina zuwa wurinka, Ina fadar wadannan abubuwa tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu.
14 Na ba su maganarka, kuma duniya ta tsane su domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.
15 Ba ina roko ka dauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga mugun nan.
16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.
17 Ka kebe su domin kanka cikin gaskiya. maganarka gaskiya ce.
18 Kamar dai yadda ka aiko ni cikin duniya, haka kuma na aike su cikin duniya.
19 Na kebe kaina gareka sabili da su, domin su ma kansu a kebe su gareka cikin gaskiya.
20 Ina addu'a ba domin wadannan kadai ba, amma har da wadanda zasu gaskata da ni ta wurin maganarsu,
21 Domin su zama daya dukansu, kamar yadda kai, ya Uba, ka ke ciki na, ni kuma na ke cikin ka. Ina roko suma su kasance a cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa ka aiko ni
22 Daukakar da ka bani, ita nake basu, domin su zama daya, kamar yadda mu ke daya;
23 ni a cikinsu, kai kuma a ciki na. Domin su kammalu cikin zama daya, domin duniya ta sani cewa ka aiko ni, kuma ka kaunace su, kamar yadda ka kaunace ni.
24 Ya Uba, ina so wadanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, domin su dubi daukakata da ka yi mani. Domin ka kaunace ni tun kafin halittar duniya.
25 Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta sanka ba, amma ni na sanka; kuma wadannan sun sani kai ne ka aiko ni.
26 Na sanar masu da sunanka, zan kuma sanar da shi domin kaunar da ka yi mani ta kasance a cikinsu, ni kuma in kasance a cikinsu,