21
1 Bayan wadannan abubuwa, Yesu ya sake bayyana kansa ga almajiran a bakin tekun Tibariya. Ga yadda ya bayyana kansa:
2 Saminu Bitrus na tare da Toma wanda ake kira Dan Tagwai, da Natana'ilu daga Kana ta kasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma wadansu almajiran Yesu biyu.
3 Saminu Bitrus yace masu, “Zani su.” sukace masa “Mu ma za mu je tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi, amma a daren nan basu kama komai ba.
4 To, gari na wayewa, sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran basu gane cewa Yesu bane.
5 Sai Yesu yace masu, “Samari, kuna da wani abinda za a ci?” Suka amsa masa sukace “A'a”.
6 Yace masu, “Ku jefa taru dama da jirgin zaku samu wasu.” Suka jefa tarunsu har suka kasa jawo shi don yawan kifin.
7 Sai almajirin nan da Yesu yake kauna yace wa Bitrus, “Ubangiji ne fa!” Da Saminu Bitrus yaji, Ashe, Ubangiji ne, yayi damara da taguwarsa, (don a tube yake), ya fada a tekun.
8 Sauran almajiran kuwa suka zo a cikin karamin jirgi, (domin basu da nisa da kasa, kamar kamu dari biyu zuwa sama), janye da tarun cike da kifi.
9 Da isowarsu gaci, sai suka ga garwashin wuta a wurin da kifi akai, da kuma gurasa.
10 Yesu ya ce masu “Ku kawo wandansu daga cikin kifin da kuka kama yanzu”.
11 Sai Saminu Bitrus ya hau, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku (153). Amma duk da yawansu, tarun bai tsage ba.
12 Yesu yace masu, “Ku zo ku karya kumallo”. Daga cikin almajiran kuwa babu wanda yayi karfin halin tambayarsa “Ko shi wanene?” Domin sunsani Ubangiji ne.
13 Yesu zo ya dauki gurasar ya ba su, haka kuma kifin.
14 Wannan shine karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan tashinsa daga matattu.
15 Da suka karya kumallon, Yesu yace wa Saminu Bitrus, “Bitrus dan Yahaya, kana kaunata fiye da wadannan?” Bitrus yace masa “I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka” Yesu yace masa “Ka ciyar da 'ya'yan tumakina”.
16 Ya sake fada masa karo na biyu, “Saminu Dan Yahaya, kana kaunata?” Bitrus Yace masa “I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka”. Yesu yace masa, “Ka lura da Tumakina”.
17 Ya sake fada masa, karo na uku, “Bitrus Dan Yahaya, kana kaunata? Sai Bitrus bai ji dadi ba domin Yesu ya fada masa karo na uku, “Kana kaunata” Yace masa, “Ubangiji ka san komai duka, ka sani ina kaunarka.” Yesu yace masa “Ka ciyar da tumaki na.
18 Hakika, hakika, Ina gaya maka, lokacin da kake kuruciyarka, kakan yi wa kanka damara, ka tafi inda ka ga dama. amma in ka tsufa, zaka mike hannuwanka wani yayi maka damara, ya kai ka inda baka nufa ba.”
19 To Yesu ya fadi haka ne domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi ga daukakar Allah. Bayan ya fadi haka, sai yace wa Bitrus, ka biyo ni.
20 Bitrus ya juya sai ya ga almajirin da Yesu yake kauna yana biye dasu; wanda ya jingina a kirgin Yesu lokacin cin jibin nan da yace “Ya Ubangiji, wanene zai bashe ka?”
21 Da Bitrus ya gan shi, yace wa Yesu “Ya Ubangiji, Me mutumin nan zai yi?”
22 Yesu yace masa, “Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka? Ka biyo ni.”
23 Wannan zance ya yadu cikin 'yan'uwa cewa, wannan almajirin ba zai mutu ba. Alhali Yesu bai cewa Bitrus, wannan almajirin ba zai mutu ba, Amma “Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka?”
24 Wannan shine almajirin da yake shaida wadannan abubuwa, wanda ya rubuta su, kuma mun tabbata shaidarsa gaskiya ne.
25 Akwai kuma sauran abubuwa da yawa wanda Yesu yayi. Idan da an rubuta kowannensu daya bayan daya, ina gaya maku, ko duniya bazata iya daukar litattafan da za a rubuta ba.