9
1 Da Yesu yana wucewa, sai ya ga wani mutum makaho tun daga haihuwa.
2 Sai almajiransa suka tambaye shi, “Mallam, wa yayi zunubi, mutumin ne ko iyayensa, har aka haife shi makaho?”
3 Yesu ya amsa, Ba mutumin ne ko iyayensa suka yi zunubi ba, amma domin aikin Allah ya bayyana a cikinsa.
4 Dole mu yi aikin wanda ya aiko ni tunda rana. Dare na zuwa inda ba mai iya yin aiki.
5 Yayinda ina duniya, ni ne hasken duniya.”
6 Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, ya tofa yawu a kasa, ya kwaba kasar da yawunsa, sai ya shafe idanun mutumin da kasar.
7 Ya ce masa, tafi, ka wanke a tafkin Siloam (ma'anarsa: aike).” Sai mutumin ya tafi, ya wanke, ya dawo yana gani.
8 Sai makwabtansa da mutanen da da suka gan shi tun can yana roko suka ce, “ Ba wannan mutum ne wanda ya ke zaune yana roko ba?”
9 Wadansu suka ce, “shi ne.” Wadansu suka ce, “A'a, amma yana kama da shi.” Amma shi ya ce, “Ni ne wannan mutum.”
10 Suka ce masa, “ To yaya aka bude maka idanu?”
11 Sai ya amsa, “Mutumin da ake ce da shi Yesu shi ya kwaba kasa ya shafa mani a idanuna ya ce mani, 'je ka kogin Siluwam ka wanke.' Sai naje na wanke, sannan na samu gani.”
12 Suka ce masa, “Ina yake?” Ya amsa, “Ban sani ba.”
13 Suka kawo mutumnin da yake makaho a da wurin farisawa.
14 A ranar asabar ne kwa Yesu ya kwaba kasa ya bude masa idanu.
15 Har yanzu farisawan suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Ya ce masu, “Ya sa mani kasa a idanuna, na wanke, kuma yanzu ina gani.”
16 Wadansu daga cikin farisawa suka ce, “Wannan mutum ba daga Allah yake ba domin ba ya kiyaye ranar Asabar. “Wadansu suka ce, “Yaya mai zunubi zai yi irin wadannan alamu?” Sai rabuwa ta shiga tsakanin su.
17 Sai suka tambayi makahon kuma, “Me kake cewa game da shi dashike ya bude maka idanu?” Makahon ya ce, “ shi annabi ne.”
18 Har yanzu kam Yahudawan basu yarda da makantarsa ba da ganin gari da ya samu, sai da suka kirayo iyayen shi wanda ya sami ganin garin.
19 Su ka tambayi iyayen, “Wannan shine yaronku da kuka ce an haife shi makaho? Yaya yanzu ya ke iya gani?”
20 Sai iyayen suka amsa masu, “Mun san wannan yaronmu ne kuma a makaho aka haife shi.
21 Yadda ya ke gani yanzu, bamu sani ba, kuma wanda ya bude masa idanu, bamu sani ba. Ku tambaye shi, ba yaro ba ne. Zai iya magana don kansa.”
22 Iyayensa sun fadi wadannan abubuwan, domin suna ji tsoron Yahudawan. Gama Yahudiyawan sun rigaya sun yarda duk wanda yace Yesu Almasihu ne, za a fitar dashi daga majami'a.
23 Domin wannan ne, iyayensa suka ce, “Ai shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”
24 Suka sake kiran mutumin dake makaho karo na biyu, suka ce masa, “Ka girmama Allah. Mu kam mun sani wannan mutum mai zunubi ne.”
25 Sai wannan mutum ya amsa, “ Ban sani ba ko shi mai zunubi ne. Abu guda daya na sani: da Ni makaho ne, amma yanzu ina gani.”
26 Sai su ka ce masa, “Me ya yi maka? Ta yaya ya bude idanunka?”
27 Ya amsa, “ Na rigaya na gaya maku, amma ba ku ji ba! Don me kuke so ku sake ji? Ko kuma kuna so ku zama almajiransa, haka ne?
28 Sai suka kwabe shi suka ce, “kai ne almajirinsa, amma mu almajiran Musa ne.
29 Mun sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum, bamu san ko daga ina ne ya zo ba.”
30 Mutumin ya amsa masu ya ce, “ Tirkashi, baku san inda ya fito ba, duk da haka shi ya bude mani idanu.
31 Mun san da cewa Allah baya jin masu zunubi, amma idan wani mai ibada ne yana kuma yin nufinsa, to yana jin sa.
32 Tunda duniya ta fara ba a taba jin cewa wani ya bude idanun wanda aka haifa makaho ba.
33 In mutumin nan ba daga Allah yake ba, ba zai iya yin komai ba.”
34 Suka amsa suka ce masa, “an haife ka cikin zunubai, yanzu kana so ka yi mana koyarwa?” Sai suka fitar da shi.
35 Yesu ya ji cewa sun fitar da shi daga majami'a. Da ya same shi sai ya ce masa, “Kana bada gaskiya ga Dan Allah?”
36 Sai ya amsa masa yace, “Wanene shi, Ubangiji, da zan bada gaskiya gare shi?”
37 Yesu yace masa, “Ai ka gan shi, shine wanda yake magana da kai.”
38 Mutumin ya ce, “Ubangiji, Na bada gaskiya.” Sai ya yi masa sujada.
39 Yesu ya ce, “ Don hukunci na zo wannan duniya domin wadanda ba su gani su gani, saboda kuma wadanda suke gani su zama makafi.”
40 Wadansu Farisawa wadanda suke tare da shi suka ji wadannan abubuwan, suka tambaye shi, “Muma makafi ne?”
41 Yesu ya ce masu, “ Inda ku makafi ne, da ba ku da zunubi, amma yanzu kun ce, 'Muna gani', don haka zunubinku ya tabbata.