12
1 Sai Yesu ya fara koyar da su da misalai. “Wani mutum ne ya yi gonar inabi ya shingen ta, ya haka ramin matse inabin, ya kuwa gina hasumayar tsaro. Ya ba wandansu manoma jinginar gonar, sa'an nan ya tafi wata kasa mai nisa.
2 Da lokaci ya yi, sai ya aika masu wani bawansa domin ya karbi wadansu daga cikin amfanin gonar.
3 Amma manoman suka kama shi, suka yin masa duka, suka kore shi hannu banza.
4 Ya sake aikar wani bawan. Shi kuma suka raunata shi aka, suka wulakanta shi.
5 Ya sake aiken wani. Shi kam, suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da wadansu da yawa, sun dodoki wadansu, suka kuma kashe wadansu.
6 Yanzu dai yana da sauran daya tak, shine kaunatacen dansa. Daga karshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ai za su bashi girma.
7 Amma manoman nan suka ce wa juna, “ai, wannan shine magajinsa, 'ku zo mu kashe shi, gadon ya zama namu.”
8 Sai suka kamo shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge.
9 To, me mai gonar inabin zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba wadansu gonar.
10 Ashe, ba ku karanta wannan nassi ba? cewa, ' Dutsen da magina suka ki, shi ne ya zama mafi mahmimanci.
11 Wannan daga Ubangiji ne, kuma ya yi dai dai a idanunmu.”'
12 Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi masalin, amma suka ji tsoron jama'a. Don haka suka kyele shi, suka tafi.
13 Suka aika masa da wadansu farisiyawa da Heridiyawa, don su sa masa tarko da kalamai cikin maganarsa.
14 Da suka zo, suka ce masa, “Malam, gaskiya kana koyar da maganar Allah sosai, ba ka nuna bambanci tsakani mutane, sai koyar da tafarkin Allah kake yi sosai. “Shin, mu biya haraji ga Kaisar, ko a a?”
15 AmmaYesu ya gane munafuncinsu, ya ce masu, “Don me kuke gwada ni? ku kawo mani dinarin in gani.”
16 Suka kawowa Yesu daya. Ya ce masu, “ Kamar waye da kuma rubutun wanene? suka ce masa, “Na Kaisar ne.”
17 Yesu ya ce, “to, ku ba Kaisar abinda yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah. Sai suka yi mamakinsa kwarai.
18 Sai Sadukiyawa suka zo wurinsa, su dake cewa babu tashin matattu. Suka tambaya shi suka ce,
19 “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba da, lallai ne dan'uwan mutumin ya auri matar, ya haifa wa dan'uwansa 'ya'ya.'
20 To an yi wadansu 'yan'uwa maza guda bakwai, na farko ya yi aure, ya mutu bai bar 'ya'ya ba.
21 Na biyu kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba 'ya'ya. Na ukun ma haka.
22 Haka dai duk bakwai din, ba wanda ya bar 'ya'ya. A karshe kuma ita matar ta mutu.
23 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai din nan sun aure ta”.
24 Sai Yesu ya ce, “Ba saboda wannan dalili ne kuka yi kuskure ba, wato don ba ku san littafin ba, kuma ba ku san ikon Allah ba?
25 Domin in an tashin daga matattu, ba a aure, ba a auraswa, amma sun zama kamar malaiku a sama.
26 Amma game da mattattun da suka tashi, ashe, ba ku taba karantawa a littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa? “Ni ne Allah na Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu'?
27 Ai, shi ba Allahn mattatu bane, amma na rayyayu ne. Hakika kun yi kuskure “.
28 Sai wani malamin attuara ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu yana ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, “Wanne Umarni ne mafi girma dukka?”
29 Yesu ya amsa yace, “ mafi girma shine, 'ku saurara ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji daya ne.
30 Sai ka kaunaci Ubangiji Allah da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka da dukkan tunaninka, da dukkan karfinka.
31 ta biyu itace, 'ka kaunaci makwabcinka kamar kanka, Ba wata doka da ta fi wadannan.''
32 Sai malamin attaura ya ce masa, “Hakika gaskiyarka malam, Allah daya ne, ba kuma wani sai shi.
33 A kaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukkan hankali, da dukkan karfi, a kuma kaunaci makwabci kamar kanka, ai ya fi dukkan hadayu na konawa.”
34 Da Yesu ya ga ya yi masa magana da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka nesa da mulkin Allah.” Bayan wannan kuma ba wanda ya sake tambayarsa wani abu.
35 Yesu ya amsa a lokacin da yake koyarwa a Haikali, ya ce “Yaya malaman attaura suke ce wa Kristi dan Dauda ne?
36 Domin Dauda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ubangiji ya ce wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na kaskantar da makiyanka'.
37 Dauda da kansa ya kira shi 'Ubangiji; To, ta yaya ya Almasihu zai zama Dan Dauda?” Babban taron jama'ar suka saurare shi da murna.
38 A koyarwa sa Yasu ya ce, “ku yi hankali da malaman attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishesu a kasuwa,
39 da kuma son wuraren zama masu daraja a haikali, da wurin bukukuwa.
40 Sun kuma kwace gidajen gwauraye, da yin doguwar addu'a, don mutane su gani. Wadanan mutanen zasu sami hukunci mai tsanani.”
41 Sai ya zauna a gaban akwatin baiko a Haikalin, yana duban yadda jama'a suke zuba kudi a ciki.
42 Wadansu masu arziki da yawa suna zuba kudi masu tsoka. Sai gwauruwa mara abin hanu ta saka anini biyu a ciki akwatin baikon.
43 Ya kira almajiransa, ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, abinda gwauruwa nan ta saka a akwatin baikon nan ya fi na sauran dukka.
44 Su duk sun bayar daga yalwa tasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta bada duk abinda take da shi.”