7
1 Farisawa suka taru wurin Yesu tare da wadansu marubuta wadda suka zo daga Urushalima.
2 Sun ga cewa wasu daga cikin almajiransa sun ci gurasa da hannuwa marasa tsabta, wato, basu wanke hannu ba,
3 (Domin Farisawa da dukan Yahudawa ba su cin abinci sai dole sun wanke hannu da kyau domin suna kiyaye al'adun dattawa.
4 Idan Farisawa suka dawo daga kasuwa, wajibi ne su yi wanka kamin su ci abinci. Akwai sauran al'adun da suke kiyayewa, kamar wanke moda, tukwane, da wasu santula na dalma, har da dakin cin abinci.)
5 Farisawa da Marubuta suka tambaye Yesu, “Don me almajiran ka basu kiyaye al'adun dattawa, domin suna cin abinci ba tare da sun wanke hannu ba?”
6 Amma ya amsa masu cewa, “Ishaya ya yi anabci akan ku masu bautan ganin ido, da ya rubuta cewa 'wadanan mutane suna girmama ni a baka amma zuciyar su tana nesa da ni.
7 Sujadar wofi suke mani suna koyar da ka'idodi na mutane a matsayin rukunansu'”.
8 Kun watsar da dokar Allah sai kuka rungumi al'adun mutane.
9 Sai yace masu, kun yi nasara wurin kau da dokokin Allah domin ku kiyaye al'adun ku na mutane.
10 Koda shike Musa ya rubuta cewa, “ka girmama Ubanka da Uwarka”, kuma, “duk wanda ya zagi Ubansa ko Uwatasa, ya cancanci mutuwa nan take”.
11 Amma kun ce, 'idan mutum ya ce wa iyayensa, “duk taimakon da ya cacanci ku samu daga guna ya zama kebabbe (wato, 'na mika wa Allah)”'.
12 Sabo da haka, kun ba shi izini kada ya yi wa Ubansa ko Uwatasa wani abu.
13 Kuna mayar da dokan Allah abin banza, sabili da al'adun ku da kuka mika masu. Wannan, da wasu abubuwa kamar haka kuke yi.”
14 Ya kara kiran taron jama'ar yace masu, “ku kasa kunne gareni, kuma ku gane.
15 Babu wani abu daga wajen mutum da zai iya gurbatar da shi har idan ya shiga cikinsa. Amma, abinda ya fita daga cikinsa shike gurbatar da shi”
16 Bari mai kunnen ji, ya ji.
17 Da Yesu ya bar taron jama'ar, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar wannan misali.
18 Sai Yesu yace, 'ashe baku da ganewa? ko baku sani cewa abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba zai iya gurbatar da shi ba,
19 domin ba zai iya kai wa cikin zuciyarsa ba, sai dai ya shiga cikin sa ya kuma fita a matsayin bayan gari a salga”. Da wannan magana, Yesu ya mayar da dukan abinci ya zama da tsabta.
20 Ya ce, abinda ke cikin mutum shike gurbatar da shi
21 Domin daga cikin mutum, kuma daga cikin zuciyarsa ne, mugun tunani, lalata, sata, kisa,
22 zina, kwadayi, mugunta, hai'inci, mugun guri, kishi, zargi, girmankai, wawanci.
23 Duk wadannan miyagun abubuwa suna fitowa ne daga cikin mutum, kuma suke gurbatar da shi.”
24 Ya tashi daga nan ya tafi shiyyar Sur da Sida. Ya shiga wani gida don baya son wani ya sani cewa yana nan, amma bai iya boyuwa ba.
25 Amma nan da nan wata mace, wadda diyarta ke da mugun ruhu-wannan mace kuwa ta ji game da Yesu sai ta zo ta durkusa a gabansa.
26 Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take. Ta roke shi da ya fitar da mugun ruhun nan daga diyarta.
27 Sai ya ce mata, “Bari a ciyar da 'ya'ya tukuna. Domin bai kamata a dauki abincin yaya a ba karnuka ba”.
28 Sai ta amsa masa cewa, “I, Ubangiji, Karnukan ma sukan ci abincin da ke fadowa daga teburin 'ya'yan.”
29 Ya ce mata, “domin kin fadi haka, kina iya ki tafi domin aljani ya fita daga diyarki.”
30 Ta koma gida sai ta iske diyarta na kwance akan gado, aljanin ya fice daga jikinta.
31 Ya sake fita daga shiyar Sur, ya biyo ta Sidon, har zuwa tekun Galili a shiyar Dikafolis.
32 Sun kawo masa wani kurma, kuma bebe ne shi, suna rokansa ya dora hanuwansa a bisansa.
33 Sai ya jawo shi daga taron jama'ar, zuwa gefe, sai ya sa hanunsa a kunuwan beben bayan ya tufa yawunsa, sannan ya taba harshensa.
34 Ya dubi sama, ya ja numfashi ya ce masa, “Ifatha”, wato, “bude!”
35 Nan da nan ya mayar masa da jinsa. abinda ya daure harshensa ya sake shi, sai ya fara magana da kyau.
36 Ya umarce su da kada su gaya wa wani. Amma duk da umarnin da yake basu, suna ta shaida shi ko'ina.
37 kuma suna ta mamaki cewa, “Yayi kowanne abu da kyau, har ya sa kurame suna jin magana, da kuma bebaye na magana.”