16
Sai Farisawa da Sadukiyawa suka zo su gwada shi suka roke shi ya nuna masu alama daga sama. Amma ya amsa ya ce masu, “Lokacin da yamma ta yi, sai ku ce, 'Za a yi yanayi mai kyau, domin sama ta yi ja,' Kuma da safe ku ce, 'Zai zama yanayi mara kyau a yau, domin sama ta yi ja ta kuma gama gari, kun san yadda za ku bayyana kammanin sararin sama, amma ba ku iya bayyana alamun lokaci ba. Mugun zamani, maciya amana suna neman alama, amma babu wata alama da za a nuna sai ta Yunusa.” Daga nan sai Yesu ya tafi. Almajiran suka zo daga wancan gefe, amma sun manta su dauki gurasa, Yesu ya ce masu, “Ku kula ku kuma mai da hankali da yisti na Farisawa da Sadukiyawa.” Sai almajiran suka fara magana da junansu suka ce, “Ko saboda bamu kawo gurasa bane.” Yesu yana sane da wannan sai ya ce, “Ku masu karancin bangaskiya, don me ku ke magana a tsakaninku cewa ko don bamu kawo gurasa bane? Ba ku gane ko tuna da gurasa guda biyar da aka ciyar da mutum dubu biyar, kuma kwando nawa kuka tara ba? 10 Ko gurasa bakwai ga mutum dubu hudu, da kuma kwanduna nawa kuka dauka ba? 11 Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa.” 12 Sa'annan suka fahimta cewa ba yana gaya masu su yi hankali da yistin da ke cikin gurasa ba ne, amma sai dai su yi lura da koyarwar Farisawa da Sadukiyawa. 13 A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, “Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake? 14 Suka ce, “Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa.” 15 Ya ce masu, “Amma ku wa kuke ce da ni?” 16 Sai Saminu Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai.” 17 Yesu ya amsa ya ce masa, “Mai albarka ne kai, Saminu dan Yunusa, don ba nama da jini ba ne ya bayyana maka wannan, amma Ubana wanda ke cikin sama. 18 Ina kuma gaya maka cewa kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikilisiya ta. Kofofin hades ba za su yi nasara da ita ba. 19 Zan ba ka mabudan mulkin sama. Duk abin da ka kulla a duniya zai zama abin da an kulla a cikin sama, kuma duk abinda ka warware a duniya a warware yake cikin sama,” 20 Sai Yesu ya umarci almajiransa kada su gaya wa kowa cewa shi ne Almasihu. 21 Daga lokacin nan Yesu ya fara gaya wa almajiransa cewa dole ne ya tafi Urushalima, ya sha wahala mai yawa a hannun dattawa, da manyan firistoci da malaman attaura, a kashe shi, a tashe shi zuwa rai a rana ta uku. 22 Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, “Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba.” 23 Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane.” 24 Sa'annan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk wanda yake so ya bi ni, lallai ne ya ki kansa, ya dauki gicciyensa, ya bi ni. 25 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi. Duk wanda ya rasa ransa domina zai same shi. 26 Domin wace riba mutum zai samu in ya sami dukan duniya ya rasa ransa? Me mutum zai iya bayarwa a maimakon ransa? 27 Domin Dan Mutum zai zo ne cikin daukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. Sa'annan ne zaya biya kowane mutum bisa ga ayyukansa. 28 Gaskiya ina gaya maku, akwai wadansun ku da ke tsaye a nan, da ba za su dandana mutuwa ba sai sun ga Dan Mutum na zuwa cikin mulkinsa.”