22
Yesu ya sake yi masu magana da misalai, yace, “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya wa dansa liyafar aure. Ya aiki bayinsa su kira wadanda aka gayyata su zo liyafar auren, amma suka ki zuwa. Sai sarkin ya sake aiken wasu bayin, yace, “Ku gaya wa wadanda aka gayyata, “Duba, na shirya liyafata. An yanka bajimaina da kosassun 'yanmarukana, an gama shirya komai. Ku zo wurin bikin auren.” Amma mutanen ba su dauki sakon da mahimmanci ba kuma suka yi tafiyarsu. Wani ga gonarsa, wani ga kasuwancinsa. Sauran kuma suka kama bayin sarkin, suka wulakanta su, suka kuma kashe su. Amma sarkin ya ji haushi. Ya aika sojojinsa, ku kashe masu kisan kan nan, ku kuma kone birnin su. Sai ya ce wa bayinsa, 'An gama shirya bikin, amma wadanda aka gayyata ba su cancanta ba. Saboda haka ku je bakin hanya ku gayyaci iyakar yawan mutanen da za ku samu zuwa bukin auren.' 10 Bayin suka tafi hanya suka tattaro dukan mutanen da suka samu, da masu kyau da marassa kyau. Zauren auren kuwa ya cika makil da baki. 11 Amma da sarkin ya zo don ya ga bakin, sai ya ga wani wanda bai sa kayan aure ba. 12 Sai sarkin ya ce masa, 'Aboki, ta yaya ka shigo nan ba tare da kayan aure ba?' Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. 13 Sai sarkin ya ce wa bayinsa, 'Ku daure mutumin nan hannu da kafa, ku jefa shi cikin duhun, inda za ayi kuka da cizon hakora.' 14 Gama mutane dayawa aka kira, amma kadan aka zaba.”' 15 Sai Farisawan suka tafi suka shirya makirci akan yadda zasu kama shi ta maganarsa. 16 Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu, “Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane. 17 To gaya mana, menene tunaninka? Ya halarta a biya haraji ga Kaisar ko a'a?” 18 Amma Yesu ya gane muguntarsu yace, “Don me kuke gwada ni, ku munafukai? 19 Ku nuna mani sulen harajin.” Sai suka kawo masa sulen. 20 Yesu yace masu, “Hoto da sunan wanene wadannan?” 21 Suka ce masa, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce masu, “To ku ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah.” 22 Da suka ji haka, suka yi mamaki. Sai suka bar shi suka tafi. 23 A ran nan sai wadansu Sadukiyawa, wadanda suka ce ba tashin matattu, suka zo wurinsa. Suka tambaye shi, 24 cewa, “Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya. 25 Akwai wasu 'yan'uwa bakwai. Na farkon yayi aure sai ya mutu. Da shike bai bar 'ya'ya ba. Ya bar wa dan'uwansa matarsa. 26 Sai dan'uwansa na biyu shi ma yayi haka, haka kuma na ukun, har zuwa dan'uwan na bakwai. 27 Bayan dukansu, sai matar ta mutu. 28 To a tashin matattu, matar wa zata zama a cikin su bakwai din? Don duk sun aure ta.” 29 Amma Yesu ya amsa yace masu, “Kun bata, domin ba ku san litattafai ko ikon Allah ba. 30 Domin a tashin matattu basu aure, ba kuma a bada su aure. Maimaikon haka, suna kama da mala'ikun sama. 31 Amma game da tashin matattu, ba ku karanta abinda Allah ya fada maku ba, cewa, 32 'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu.” 33 Da taron suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa. 34 Amma da Farisawan suka ji cewa Yesu ya kure Sadukiyawa, sai suka tattara kansu. 35 Daya daga cikinsu, masanin shari'a, yayi masa tambaya, yana gwada shi- 36 “Mallam, wace doka ce mafi girma a cikin shari'a?” 37 Yesu yace masa, “Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.' 38 Wannan itace babbar doka ta farko. 39 Doka ta biyu kuma kamar ta take- 'Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.' 40 Akan wadannan dokoki ne dukkan shari'a da annabawa suka rataya.” 41 Yayin da Farisawa suke tattare wuri daya, Yesu yayi masu tambaya. 42 Yace, “Me kuke tunani game da Almasihu? Shi dan wanene?” Suka ce masa, ''Dan Dauda ne.” 43 Yesu yace masu, “To ta yaya kuma Dauda cikin Ruhu ya kira shi Ubangiji, yana cewa, 44 “Ubangiji ya cewa wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na mai da makiyanka matakin sawayenka.” 45 Idan Dauda ya kira Almasihu 'Ubangiji,' ta yaya ya zama dan Dauda?” 46 Ba wanda ya iya bashi amsa, ba kuma wanda ya kara yi masa tambayoyi tun daga wannan rana.