24
Yesu ya fita daga cikin haikalin ya kama hanyar sa. Almajiran sa suka zo suna nuna masa ginin haikali. Amma ya amsa masu yace, “kun ga dukkan wadannan abubuwan? Ina gaya maku gaskiya, ba ko dutse daya da za'a bari akan dan'uwansa wanda ba za'a rushe shi ba.” Yayin da ya zauna a kan dutsen zaitun, almajiran sa suka zo wurin sa a boye suka ce, “me zai zama alamar zuwanka da kuma na karshen duniya?” Yesu ya amsa yace dasu, “Ku kula kada wani yasa ku kauce.” Gama da yawa za su zo da sunana. Za su ce, “ni ne almasihu,” kuma za su sa da yawa su kauce. Za ku ji labarin yake-yake da kuma shelar yake-yake. Ku kula kar ku tsorata, domin dole abubuwan nan su faru; amma karshen dai tukunna. Gama al'umma zata tayarwa al'umma, kuma mulki zai tayarwa mulki. Za'a yi yunwa da girgizar kasa a wurare dabam dabam. Amma dukkan wadannan farkon ciwon haihuwa ne kawai. Bayan haka za'a bada ku ga tsanani a kuma kashe ku. Dukkan al'ummai za su tsane ku saboda sunana. 10 Daga nan da yawa za su yi tuntube, kuma su ci amanar juna, su kuma tsani juna. 11 Annabawan karya da yawa za su taso kuma susa da yawa su kauce. 12 Domin mugunta zata ribambanya, kaunar masu yawa zata yi sanyi. 13 Amma duk wanda ya jure har karshe, zai sami ceto. 14 Za'a yi wa'azin wannan bisharar mulkin a dukkan duniya don ya zama shaida akan dukkan al'ummai. Daganan karshen zai zo. 15 Don haka, idan kun ga abin kyama mai lalatarwa, wanda Annabi Daniyel ya yi maganar sa, Ya tsaya a wuri mai tsarki (bari mai karatu ya fahimta), 16 bari wadanda ke yahudiya su gudu zuwa kan duwatsu, 17 Bari wanda yake kan bene kada ya sauko don daukar wani abu a cikin gidansa, 18 kuma wanda yake gona kar ya dawo gida domin daukar babbar rigarsa. 19 Amma kaito ga wadanda suke dauke da yaro, ko masu shayarwa a wannan kwanakin! 20 Ku yi addu'a kada gudun ku ya zama lokacin hunturu, ko ranan asabaci. 21 Domin za'ayi tsanani mai girma, wanda ba'a taba yin irin shi ba, tun farkon duniya har ya zuwa yau, a'a ba za ayi irin shi ba kuma. 22 In ba don an rage kwanakin ba, da ba mahalukin da zai tsira. Amma albarkacin zababbun, za a rage kwanakin. 23 Sa'annan idan wani yace maku, duba, “ga Almasihu a nan!” ko, “ga Almasihu a can!” kar ku gaskata. 24 Gama annabawan karya da almasihan karya za su zo suna nuna alamu da al'ajibai, don su yaudari masu yawa zuwa ga bata, in ya yiwuma har da zababbun. 25 Kun gani, na gaya maku kafin lokacin ya zo. 26 Saboda haka, idan suka ce maku, “ga shi a jeji,” kar ku je jejin. Ko, “ga shi a can cikin kuryar daki,” kar ku gaskata. 27 Yadda walkiya ke haskakawa daga gabas zuwa yamma, haka nan zuwan Dan mutum zai zama. 28 Duk inda mushe yake, nan ungulai suke taruwa. 29 Amma nan da nan bayan kwanakin tsananin nan, rana za ta duhunta, wata kuma ba zai ba da haskensa ba, taurari kuma za su fado daga sama, ikokin sammai za su girgiza. 30 Sa'annan alamar Dan Mutum za ta bayyana a sararin sama, kuma dukkan kabilun duniya za su yi bakin ciki. Za su ga Dan Mutun na zuwa a gajimarai da iko da daukaka mai girma. 31 Zai aiki mala'ikunsa, da karar kaho mai karfi, kuma za su tattara dukkan zababbu daga dukkan kusurwoyi hudu, daga karshen sararin sama har zuwa wani karshen. 32 Kuyi koyi da itacen baure. Da zaran reshen sa ya yi toho ya fara bada ganye, za ku sani bazara ta kusa. 33 Haka kuma, idan kun ga dukkan wadannan abubuwa, ya kamata ku sani, Ya yi kusa, ya na bakin kofa. 34 Ina gaya maku gaskiya, wannan zamanin ba zai wuce ba, sai dukkan wadannan abubuwan sun faru. 35 Sama da kasa za su shude, amma kalmomina ba za su shude ba. 36 Amma game da ranan nan ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai Uban kadai. 37 Kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka zai zama game da zuwan Dan Mutum. 38 A wadannan kwankin kafin zuwan ruwan tsufana suna ci suna sha, suna aure suna aurarwa har ranar da Nuhu ya shiga jirgin, 39 ba su san kome ba har ruwan ya zo ya cinye su_ haka ma zuwan Dan Mutun zai zama. 40 Sa'annan mutane biyu zasu kasance a gona za a dauke daya, a bar daya a baya. 41 Mata biyu na nika a manika za a dauke daya, za a bar dayar. 42 Don haka sai ku yi zaman tsaro, domin baku san ranar da Ubangijinku zai zo ba. 43 Amma ku san wannan, idan maigida ya san lokacin da barawo zai zo, zai zauna a shirye ba zai bar gidan sa har a balle a shiga ba. 44 Don haka sai ku shirya, domin Dan Mutum zai zo a sa'ar da ba ku yi zato ba. 45 To wanene amintaccen bawannan mai hikima, wanda maigidan sa ya sa ya kula mar da gida, domin ya ba su abinci a kan lokaci? 46 Mai albarka ne bawan, da mai gidan zai same shi a kan aikin sa a lokacin da ya dawo. 47 Ina gaya maku gaskiya mai gidan zai dora shi a kan dukkan a binda yake da shi. 48 Amma idan mugun bawa ya ce a zuciyarsa, “maigida na ya yi jinkiri,” 49 sai ya fara dukan sauran barorin, ya yi ta ci da sha tare da mashaya, 50 uban gidan bawan zai dawo a ranar da bawan bai zata ba, a lokacin da bai sani ba. 51 Uban gidansa zai datsa shi biyu, karshen sa zai zama daidai da na munafukai, za a sashi inda a ke kuka da cizon hakora.