28
Da daddare ranar Asabaci, rana ta fari ga mako ta fara gabatowa, Maryamu Magadaliya da daya Maryamun suka zo don su ziyarci kabarin. Sai aka yi girgizar kasa mai karfi, saboda mala'ikan Ubangiji ya sauko daga sama ya kuma murgine dutsen ya zauna a kai. Kamanninsa kamar walkiya, tufafinsa kuma fari fat kamar suno. Masu tsaron suka razana don tsoro suka zama kamar matattun mutane. Mala'ikan ya yi wa matan magana cewa, “Kada ku ji tsoro, nasan kuna neman Yesu wanda aka gicciye. Baya nan, amma ya tashi kamar yadda ya fada. Ku zo ku ga wurin da aka kwantar da shi. Ku hanzarta ku gaya wa almajiransa, 'Ya tashi daga matattu. Duba, ya tafi Galili, can zaku same shi.' Gashi ni kuwa na fada maku.” Matan suka yi hanzari suka bar kabarin da tsoro da murna, suka ruga domin su sanar wa almajiransa. Sai ga Yesu ya tare su, yace masu, “A gaishe ku.” Sai matan suka kama kafar sa, suka kuma yi masa sujada. 10 Sai Yesu yace masu, “Kada ku ji tsoro. Ku je ku fada wa 'yan'uwana su je Galili. Can zasu ganni.” 11 Sa'adda matan suke tafiya, sai wadansu masu tsaro suka shiga gari suka fada wa Shugabanin Firistoci dukan abin da ya faru. 12 Firistocin suka hadu da dattawa suka tattauna al'amarin, sai suka bada kudi masu yawa ga sojojin 13 Sukace masu, “Ku gaya wa sauran cewa, “Almajiran Yesu sun zo da daddare sun sace gangar jikinsa lokacin da muke barci.” 14 Idan wannan rahoto ya isa wurin gwamna, za mu lallashe shi mu ja hankalinsa mu raba ku da damuwa.” 15 Sai sojojin suka karbi kudin suka yi abinda aka umarcesu. Wannan rahoto ya bazu a tsakanin Yahudawa, ya ci gaba har zuwa yau. 16 Amma almajiran sha daya suka tafi Galili, kan dutsen da Yesu ya umarcesu. 17 Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma wadansu suka yi shakka. 18 Yesu ya zo wurin su ya yi masu magana, yace, “Dukan iko dake sama da kasa an ba ni. 19 Sai kuje ku almajirantar da dukan al'ummai. Kuna yi masu baftisma cikin sunan Uba da na Da da na Ruhu Mai Tsarki. 20 Ku koya masu su kiyaye dukan abin da na umarce ku. Duba, ni kuma kullum ina tare da ku har karshen zamani.”