11
1 Sai na ce, Allah ya ki mutanensa ne? Ba zai taba yiwuwa ba. Domin ni ma ba-Isra'ile ne, na zuriyar Ibrahim, a kabilar Bilyaminu.
2 Allah bai ki mutanen sa da ya ke da rigyasaninsu ba. Ko kun san abin da nassi ya ce game da Iliya, yadda ya kai karar Isra'ila a gaban Allah?
3 Ya ce, ''Ubangiji, sun kashe annabawanka, sun rushe alfarwanka kuma, Ni kadai ne na rage, ga shi suna neman su kashe ni.''
4 Amma wacce amsa ce Allah ya ba shi? Ya ce, ''Ina da mutane dubu bakwai da na kebe don kaina, da ba su taba rusuna wa Ba'al ba.''
5 Ban da haka ma, ban da haka ma a wannan lokacin akwai sauran zabe na alheri.
6 Amma tun da ta wurin alheri ne, ba ga ayyuka ba. In ba haka ba, alheri ba zai zama alheri ba kenan.
7 Sai kuma me? Abin da Isra'ila ke nema, ba su samu ba, amma zababbun sun same shi, saura kuma sun taurare.
8 Kamar yadda yake a rubuce, ''Allah ya ba su ruhun rashin fahimta, ga idanu amma ba za su gani ba, ga kunnuwa amma ba za su ji ba, har zuwa wannan rana.''
9 Dauda kuma ya ce, ''bari teburinsu ya zama taru, da tarko, ya zama dutsen tuntube da abin ramako a gare su.
10 Bari idanunsu ya duhunta domin kada su gani; bayansu kuma a duke kullum.''
11 Na ce, ''sun yi tuntube domin su fadi ne?'' Kada abu kamar haka ya faru. A maimakon haka, juyawa baya da suka yi ya sa, ceto ya zo ga Al'ummai, domin ya sa su kishi.
12 Idan yanzu juyawa baya da sun yi ya zama arziki ga duniya, rashin su kuma arziki ga Al'ummai, yaya kwatancin girmansa zai kasance in sun zo ga kammala?
13 Yanzu ina magana da ku ku da ke Al'ummai. Tunda yake ni ne manzo ga Al'ummai, ina kuma fahariya cikin hidimata.
14 Yana yiwuwa in sa ''yan'uwa na kishi, domin mu ceci wadansu su.
15 Idan kinsu ya kawo sulhuntawa ga duniya, Karbarsu kuma zata zama yaya? Zata zama rai ne daga mutuwa.
16 'ya'yan farko sunan haka ma kakkabensu yake, Idan saiwar itace na nan, haka ma rassan za su zama.
17 Amma idan an karye wasu daga cikin rassan, idan ku rassan zaitun na ainihi ne, da aka samu daga cinkinsu, kuma idan kuna da gado tare da su, acikin saiwar itacen zaitun din.
18 Kada ku yi fahariya a kan rassan. Amma idan kuka yi fahariya to ba ku bane masu karfafa saiwar amma saiwar ce ke karfafa ku.
19 Kana iya cewa, ''An karye rassan domin a same ni a ciki.''
20 Wannan gaskiya ne! Saboda rashin bangaskiyarsu ne ya sa aka karye su daga rassan, amma ku tsaya da karfi acikin bangaskiyarku. Kada ku dauki kanku fiye da yadda ya kamata, amma ku ji tsoro.
21 Domin idan Allah bai bar ainihin rassan ba, to ba zai bar ku ba.
22 Ku duba yadda irin ayyuka masu tsananni na Allah. Ta daya hannun kuma, tsanannin kan zoa kan Yahudawa wadanda suka fadi. Har 'ila yau jinkai Allah ya zo maku, idan kun cigaba cikin alherinsa baza a sare ku ba. Amma in kun ki za a sare ku.
23 Hakanan, idan ba su ci gaba cikin rashin bangaskiyarsu ba, za a maida su cikin itacen. Domin Allah zai iya sake maida su.
24 Idan an yanke ka daga itacen zaitun da ke na jeji, har ya yiwu an hada ka cikin itacen zaitun na ainihi, yaya kuma wadannan Yahudawa wadanda sune ainihin rassan, da za'a maido cikin zaitun da ke na ainihi?
25 Yan'uwa, ba na so ku kasance cikin duhu a game da wannan asirin, domin kada ku zama da hikima cikin tunaninku. Wannan asirin shine cewa wannan taurarewa ta faru a Isra'ila, har sai da Al'ummai suka shigo ciki.
26 Ta haka dukan Isra'ila za su tsira, kamar yadda yake a rubuce: ''Daga cikin Sihiyona mai Kubutarwa zai fito; Zai kawar da kazanta daga cikin Yakubu.
27 Wannan zai zama alkawarina da su, sa'adda na kawar da zunubansu.''
28 A wani bangaren kuma game da bishara, su makiya ne amamadinku, ta wani fannin kuma bisa ga zabin Allah su kaunattatu ne saboda ubanni.
29 Domin baye-baye da kiran Allah basa canzawa.
30 Domin ku ma da ba ku yin biyayya ga Allah, amma yanzu kun sami jinkai saboda rashin biyayyarsu.
31 Ta wannan hanyar dai, wadannan Yahudawan sun zama marasa biyayya. Sakamakon haka shine ta wurin jinkan da aka nuna maku, suma su samu jikai yanzu.
32 Domin Allah ya rufe kowa ga rashin biyayya, domin ya nuna jinkai ga kowa.
33 Ina misalin zurfin wadata da kuma hikima da sani na Allah! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban a bincika, hanyoyinsa kuma sun fi gaban ganewa!
34 Don wanene ya san tunanin Ubangiji? Wanene kuma ya zama mai bashi shawara?
35 Ko kuma, wanene ya fara ba Allah wani abu, domin a biya shi?''
36 Daga wurinsa ne, ta wurinsa ne kuma, a gare shi ne kuma dukan abu suka fito. A gare shi daukaka ta tabbata har abada. Amin.