9
Gaskiya ne nake gaskiya nake fada cikin Almasihu. Ba karya nake yi ba. Lamirina, na shaida a cikin Ruhu Mai Tsarki. cewa ina da matukar bakin-ciki da takaici marar karewa a zuciyata. Dama ace, a la'anta ni, in rabu da Almasihu saboda 'yan'uwana, wato dangina da suke zuriyata bisa ga jiki. Sune Isra'ilawa, sun sami karbuwa, da daukaka, da baiwar shari'a, da yi wa Allah sujada, da alkawarai. Dukkan ubanni nasu ne daga cikinsu Almasihu ya fito bisa ga jiki- wanda shi ke Allah bisa kowa. Yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin. Amma ba wai alkawarin Allah ya kasa ba ne, ba dukkan Isra'ilawa ne suke Isra'ilawa na gaskiya ba. Haka nan, ba dukkan zuriyar Ibrahim ne 'ya'yansa ba. Amma ''ta wurin Ishiyaku ne za'a kira zuriyarka.'' Yana nuna mana cewa ba 'ya'yan jiki su ne 'ya'yan Allah ba. Amma 'ya'yan alkawari ne ake kirga su, kuma aka kebe su. Wanna ce kalmar alkawari, ''badi warhaka zan dawo, Saratu kuwa zata sami da.'' 10 Amma ba wannan kadai ba, bayan Rifkatu ta dauki ciki daga gun mijinta, ubammu Ishiyaku. 11 Yaran nan kafin ma a haife su, balle ma a ce sun yi wani abu mai kyau ko laifi, saboda zaben da Allah yayi, bai danganta da abin da suka yi ba, ko don aiki ba, amma don shine mai kira— 12 kamar yadda Ya ce, mata, “babban zaya yiwa karamin bauta,'' haka nassi yace, 13 ''Kamar yadda aka rubuta: “Yakubu na ke kauna, amma Isuwa na ki shi.” 14 To me zamu ce kenan? Allah ya yi rashin adalci kenan? Ko kadan. 15 Gama ya ce wa Musa, ''Ina nuna jinkai ga wanda zan yi wa jinkai, zan ji tausayi ga wanda zan tausaya masa.'' 16 Saboda haka, ba don wanda ke da aniya ba ne, ko kuwa wanda yake kokari ba, amma saboda Allah mai nuna jinkai. 17 Gama nassi ya ce da Fir'auna, '' Saboda wannan dalilin ne, na tada kai, don in nuna ikona mai karfi a kanka, don sunana ya yadu ga dukkan duniya.'' 18 Ta haka Allah ya nuna jinkansa ga wanda ya so, ya taurarar da zuciyar wanda ya ga dama. 19 Za kuce mani, to don me, ''Yake kama mu da llaifi? Wa ya taba yin jayayya da nufinsa?'' 20 In ma mun duba, kai mutum wanene kai da zaka ja da Allah? Ko abin da aka gina zai ce wa magininsa, ''Don me yasa ka ginani haka?'' 21 Ko maginin ba shi da iko akan yimbu daya da zai gina tukunya mai daraja, wata kuma tukunyar don kowanne irin aiki? 22 In ace Allah, dake niyyar nuna fushinsa da ikonsa, ya sanu, sai ya jure da matukar hakuri mai yawa da tukwanen fushi da ya shirya don hallakarwar fa? 23 To ko ma ya yi haka don ya nuna yalwar daukakarsa da take dauke da alheri, wanda ya shirya don daukakarsa tun farko? 24 Zai yiwu ma ya yi haka ne domin mu, mu da ya kira, ba ma daga cikin Yahudawa kadai ba, amma har ma daga cikin al'ummai? 25 Kamar yadda ya ce a cikin littafin Yusha'u: ''zan kira wadanda ba mutanena ba mutanena, da kuma kaunatattunta wadanda ba kaunatattu ba. 26 Zai zama kuma a inda aka ce da su, “ku ba mutanena bane, za a kisa su 'ya'yan Allah mai rai.”' 27 Ishaya ya yi kira game da Isra'ila, ''in a ce yawan 'ya'yan Isra'ila zasu zama kamar yashi a bakin teku, ragowarsu ne kawai za su sami ceto. 28 Ubangiji zai tabbatar da cikar kalmarsa a duniya, ba kuwa da dadewa ba. 29 Yadda Ishaya ya rubuta ada, ''In da ba Ubangiji mai runduna bai bar mana zuriya ba, da zamu zama kamar Saduma, da kuma an maida mu kamar Gomarata. 30 To me za mu ce kenan? Ko al'ummai, da ba sa neman adalci, sun samu adalci ta wurin bangaskiya. 31 Amma Isra'ila, wadanda suka nemi adalcinsu ta wurin shari'a, ba su kai ga gaci ba. 32 To don me? don ba su neme shi da bangaskiya ba, amma ta ayyuka. Sun yi tuntube a kan dutse da zai sa laifi. 33 Kamar yadda aka rubuta, “Ga, shi na ajiye dutse a kan Sihiyona dutsen tuntube mai sa laifi. Ga wanda ya bada gaskiya gare shi ba zai ji kunya ba.”