21
1 Sai na ga sabuwar sama da sabuwar duniya, domin sama ta fari da duniya ta fari sun shude, ba kuma teku.
2 Na ga birni mai tsarki, sabuwar Urushalima, wadda ta sauko kasa daga sama wurin Allah, shiryayya kamar amaryar da aka yi wa ado domin mijinta.
3 Na ji babbar murya daga kursiyinta na cewa, “Duba! Mazaunin Allah yana tare da 'yan adam, zai zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kuma da kansa zai kasance tare da su ya kuma zama Allahnsu.
4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu, kuma babu sauran mutuwa, ko bakinciki, ko kuka, ko azaba. Abubuwan da sun shude.
5 Shi wanda yake zaune a kan kursiyin ya ce, “Duba! Na maida kome ya zama sabo.” Ya ce, “Ka rubuta wannan domin wadannan kalmomi amintattu ne da gaskiya”.
6 Ya ce mani, “Wadannan abubuwan an gama! Ni ne Alpha da Omega, farko da karshe. Ga mai jin kishi, zan bashi kyauta daga mabulbular ruwan rai.
7 Wanda ya ci nasara, zai gaji wadannan abubuwa, ni kuma zan zama Allahnsa, shi kuma ya zama da na.
8 Amma ga matsorata, da marasa bangaskiya, da masu kazanta, da masu kisan kai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da dukan makaryata, mazaunin su zai kasance cikin tafki mai ci da farar wuta. Mutuwa ta biyu kenan.”
9 Daya daga cikin mala'ikun bakwai ya zo wurina, wanda yake dauke da tasoshi bakwai cike da annobai bakwai na karshe, yace, “Zo nan. Zan nuna maka amarya, matar Dan Rago”.
10 Sai ya dauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsawo ya nuna mani birni mai-tsarki, Urushalima, tana saukowa daga cikin sama daga wurin Allah.
11 Urushalima tana da daukakar Allah, shekinta yana kama da dutse mai tamani, sai kace dutsen yasfa, garau kamar karau.
12 Tana da babban garu mai tsawo, da kofofi goma sha biyu, da mala'iku goma sha biyu a kofofin. Akan kofofin an rubuta sunayen kabilu sha biyu na 'ya'yan Isra'ila.
13 A gabas akwai kofofi uku, a arewa kofofi uku, a kudu kofofi uku, da kuma yamma kofofi uku.
14 Garun birnin yana da harsashin gini goma sha biyu, a bisansu akwai sunaye goma sha biyu na manzanni goma sha biyu na Dan Rago.
15 Shi wanda yayi magana dani yana da sandan awo na zinariya domin ya auna birnin, da kofofinsa, da garunsa.
16 Birnin; da tsawonsa da fadinsa iri daya ne. Ya gwada birnin da sandar awo, mil dubu sha biyu a tsaye (fadinsa, da tsawonsa, da tsayinsa duka daya ne)
17 Ya kuma gwada garunsa, kamu 144, bisa ga gwajin 'yan adam (wanda shine ma'aunin mala'ika).
18 An gina garun da Yasfa birnin kuma da sahihiyar zinariya, mai kama da madubi mai kyalli.
19 An kawata harsashin garun da kowanne irin dutse mai tamani. Na fari yasfa, na biyu saffir, na uku agat, na hudu emerald,
20 na biyar Onis, na shida sardiyus, na bakwai kirisolat, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofaras, na sha daya yakinta, na sha biyu kuma ametis.
21 Kofofi goma sha biyu lu'u-lu'ai ne goma sha biyu; kowacce daya a cikin kofofin daga lu'u-lu'u daya aka yi shi. Titunan birnin kuwa zinariya ce sahihiya, sai kace madubi garau.
22 Ban ga haikali a cikin birnin ba, gama Ubangiji Allah Mai iko duka da Dan Ragon su ne haikalinsa.
23 Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi gama daukakar Allah ta haskaka shi, kuma fitilarsa Dan Rago ne.
24 Al'ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin. Sarakunan duniya kuma za su kawo daukakarsu cikinsa.
25 Kofofinsu kuma ba za a rufe su da rana ba, babu dare kuma a can.
26 Za su kawo daukaka da darajar al'ummai a cikinsa,
27 babu wani abu mai kazanta da zai taba shiga cikinsa. Ko wanda yake aikata abin kunya da karya, sai wadanda an rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Dan Rago kadai.