Wasikar Bulus Manzo Ta Biyu Zuwa Ga Timoti
1
1 Bulus, manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai da ke cikin Almasihu Yesu,
2 zuwa ga Timoti, kaunataccen da: Alheri, jinkai, da salama daga Allah Uba da Almasihu Yesu Ubangijinmu.
3 Na gode wa Allah, wanda na ke bautawa tun daga kakannina, da lamiri mai tsabta, sa'adda na ke tuna wa da kai cikin addu'o'ina koyaushe (dare da rana).
4 Sa'adda na tuna da hawayenka, na yi marmarin ganinka, saboda in cika da farin ciki.
5 An tunashshe ni game da sahihiyar bangaskiyarka, wadda ta samo asali daga kakarka Loyis da mahaifiyarka Afiniki. Na kuma tabbata ta na zaune a cikinka.
6 Wannan shine dalilin da ni ke tunashshe ka cewa ka sake rura baiwar Allah da ke cikinka wadda ka samu sa'adda na dibiya maka hannuwana.
7 Domin Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, amma na iko da kauna da kamun kai.
8 Saboda haka kada ka ji kunyar shaida ga me da Ubangijinmu, ko ni, Bulus, daurarrensa. Maimakon haka, ka zama a shirye ka sha wahala domin bishara bisa ga ikon Allah.
9 Allah ne ya cecemu kuma ya kira mu da kira mai tsarki. Ya yi wannan, ba ta wurin ayyukanmu ba, amma ta wurin shirinsa da alherinsa. Ya ba mu wadannan abubuwan a cikin Almasihu Yesu kafin farkon zamanai.
10 Amma yanzu an bayyana ceton Allah ta wurin bayyanuwar mai cetonmu Almasihu Yesu. Almasihu ne ya kawo karshen mutuwa ya kuma kawo rai marar karshe da ya bayyana ta wurin bishara.
11 Domin wannan, an zabe ni mai wa'azi, manzo da mallami zuwa ga al'ummai.
12 Domin wannan dalili na ke shan wahalar wadannan abubuwa. Amma ban ji kunya ba, domin na san shi, wanda na gaskanta. Na sakankance zai iya adana abinda na mika masa har zuwa ranan nan.
13 Ka adana misalin amintattun sakwanni da ka ji daga gare ni, ta wurin bangaskiya da kauna da ke cikin Almasihu Yesu.
14 Abu mai kyau da Allah ya danka maka, ka tsare shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da ke zaune a cikinmu.
15 Ka dai sani, dukkan wadanda su ke zama a Asiya sun juya mani baya. A cikin kungiyar akwai Fijalas da Harmajanas.
16 Bari Ubangiji ya yi wa iyalin Onisifaras jinkai, domin ya na yawan yi mani hidima, kuma ba ya jin kunyar sarkata.
17 Maimakon haka, sa'adda ya ke a Roma, ya neme ni da kokarin gaske, ya kuma same ni.
18 Bari Ubangiji ya sa, ya sami jinkai daga gare shi a wannan rana. Dukkan hanyoyin da ya taimake ni a kasar Afisa, kun sani sarai.