50
Zunubin Isra’ila da kuma biyayyar bawa
Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ina takardar shaida na saki mahaifiyarka daga aure
wadda na kora?
Ko kuwa ga wanda mutumin da nake bin bashi ne
na sayar da kai?
Saboda zunubanka aka sayar da kai;
saboda laifofinka ne ya sa aka kori mahaifiyarka.
Sa’ad da na zo, me ya sa babu kowa?
Sa’ad da na yi kira, me ya sa babu wani da ya amsa?
Hannuna ya kāsa ne sosai don fansarka?
Na rasa ƙarfin kuɓutar da kai ne?
Ta wurin tsawatawa kawai na busar da teku,
na mai da koguna hamada;
kifayensu duk sun ruɓe saboda rashin ruwa
suka kuma mutu saboda ƙishi.
Na suturar da sararin sama da duhu
na kuma mai da tsummoki abin rufuwarsa.”
 
Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni,
don in san maganar da za tă ƙarfafa gajiyayye.
Ya farkar da ni da safe,
ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa.
Ubangiji Mai Iko Duka ya buɗe kunnuwana,
kuma ban yi tayarwa ba;
ban ja da baya ba.
Na ba da bayana ga masu dūkana,
kumatuna ga masu jan gemuna;
ban ɓoye fuskata
daga masu ba’a da masu tofa mini miyau ba.
Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni,
ba zan sha kunya ba.
Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara,
na kuma sani ba zan sha kunya ba.
Gama shi da zai tabbatar da ni, marar laifi ne yana kusa.
Wane ne zai kawo ƙararraki game da ni?
Bari mu je ɗakin shari’a tare!
Wane ne mai zargina?
Bari yă kalubalance ni!
Ubangiji Mai Iko Duka ne zai taimake ni.
Wane ne zai iya tabbatar da ni mai laifi?
Duk za su koɗe kamar riga;
asu za su cinye su.
 
10 Wane ne a cikinku yake tsoron Ubangiji
yana kuma yin biyayya ga maganar bawansa?
Bari wanda yake tafiya cikin duhu,
wanda ba shi da haske,
ya dogara a sunan Ubangiji ya kuma dogara ga Allahnsa.
11 Amma yanzu fa, dukanku waɗanda kuke ƙuna wuta
kuna kuma tanada wa kanku fitilu masu ci,
ku je ku yi tafiya a cikin hasken wutarku
da na fitilun da kuka ƙuna.
Abin da za ku karɓa ke nan daga hannuna.
Za ku kwanta a cikin azaba.