51
Madawwamin ceto domin Sihiyona
“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuna neman adalci
kuke kuma neman Ubangiji.
Dubi dutse daga inda aka yanke ku
da kuma mahaƙar duwatsu inda aka fafe ku;
dubi Ibrahim, mahaifinku,
da Saratu, wadda ta haife ku.
Sa’ad da na kira shi kaɗai ne,
na kuma albarkace shi na kuma mai da shi da yawa.
Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona
zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta;
zai sa hamadanta ta zama kamar Eden,
ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji.
Za a sami farin ciki da murna a cikinta,
godiya da ƙarar rerawa.
 
“Ku kasa kunne gare ni, mutanena;
ku ji ni, al’ummata.
Doka za tă fito daga gare ni;
shari’ata za tă zama haske ga al’ummai.
Adalcina na zuwa da sauri,
cetona yana a kan hanya,
hannuna kuma zai kawo adalci ga al’ummai.
Tsibirai za su dube ni
su kuma jira da sa zuciya don hannuna.
Ku daga idanunku zuwa sammai
ku dubi duniya a ƙasa;
sammai za su ɓace kamar hayaƙi,
duniya za tă shuɗe kamar riga
mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje.
Amma cetona zai dawwama har abada,
adalcina ba zai taɓa kāsa ba.
 
“Ku ji ni, ku da kuka san abin da yake daidai,
ku mutanen da kuke da dokata a zukatanku.
Kada ku ji tsoron ba’ar da mutane suke yi
ko ku firgita saboda zargin da suke yi.
Gama asu za su cinye su kamar riga;
tsutsotsi za su cinye su kamar ulu.
Amma adalcina zai dawwama har abada,
cetona har dukan zamanai.”
 
Ka tashi, ka tashi! Ka yafa wa kanka ƙarfi,
Ya hannun Ubangiji;
ka farka, kamar a kwanakin da suka wuce,
kamar a zamanai na dā.
Ba kai ba ne wanda ya yayyanka Rahab gunduwa-gunduwa,
wanda ya soki dodon ruwan nan?
10 Ba kai ba ne ka busar da teku,
ka busar da ruwan zurfafa masu girma,
wanda ya yi hanya a cikin zurfafan teku
saboda fansassu su ƙetare?
11 Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo.
Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi;
madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani.
Murna da farin ciki zai cika su,
baƙin ciki da nishi zai ɓace.
 
12 “Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku.
Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa,
’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai,
13 har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku,
wanda ya shimfiɗa sammai
ya kuma kafa harsashen duniya,
har kuna zama da tsoro kowace rana
saboda fushin masu zalunci,
waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka?
Gama ina fushin mai zalunci?
14 Ba da daɗewa za a ’yantar da ’yan kurkuku;
ba za su mutu a kurkuku ba,
ba kuwa za su rasa abinci ba.
15 Gama ni ne Ubangiji Allahnku,
wanda ya dama teku domin raƙumansa su yi ruri,
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
16 Na sa maganata a bakinka
na kuma rufe ka da inuwar hannuna,
Na shimfiɗa sammai,
na kafa harsashen duniya,
na kuma ce wa Sihiyona, ‘Ku mutanena ne.’ ”
Kwaf na fushin Ubangiji
17 Ki farka, ki farka!
Ki tashi, ya Urushalima,
ke da kika sha daga hannun Ubangiji
kwaf na fushinsa,
ke da kika shanye har ƙasar kwaf
kwaf da ya sa mutane suna tangaɗi.
18 Cikin dukan ’ya’yan da ta haifa;
cikin dukan ’ya’yan da ta yi reno
babu wani da zai kama hannunta.
19 Waɗannan masifu riɓi biyu sun auko miki,
wa zai ta’azantar da ke?
Lalaci da hallaka, yunwa da takobi,
wa zai ƙarfafa ki?
20 ’Ya’yanki sun sume;
sun kwanta kusurwar kowane titi,
kamar barewar da aka kama da tarko.
Sun cika da fushin Ubangiji
da kuma tsawatawar Allahnki.
 
21 Saboda haka ki ji wannan, ke mai wahala,
wadda ta bugu, amma ba da ruwan inabi.
22 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
Allahnki, wanda ya kāre mutanensa,
“Duba, na ƙwace daga hannunki
kwaf da ya sa ki tangaɗi;
daga wannan kwaf, kwaf na fushina,
ba za ki ƙara sha ba.
23 Zan sa shi a hannuwan masu gwada miki azaba,
waɗanda suke ce miki,
‘Fāɗi rubda ciki don mu iya taka a kanki.’
Kika kuma mai da bayanki kamar ƙasa,
kamar titin da ake takawa a kai.”