52
1 Ki farka, ki farka, ya Sihiyona,
ki sanya wa kanki ƙarfi.
Ki sa rigarki na daraja,
Ya Urushalima, birni mai tsarki.
Marasa kaciya da maƙazanta
ba za su shi cikinki ba.
2 Ki kakkaɓe ƙurarki;
ki tashi, ki zauna a kursiyinki, ya Urushalima.
Ki ’yantar da kanki daga sarƙoƙi a wuyanki,
Ke kamammiyar Diyar Sihiyona.
3 Gama ga abin Ubangiji yana cewa,
“An sayar da ke ba da kuɗi ba,
kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.”
4 Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“Da farko mutanena suka gangara zuwa Masar don su zauna;
a baya-bayan nan, Assuriya sun zalunce su.
5 “Yanzu kuma me nake da shi a nan?”
In ji Ubangiji.
“Gama an kwashe mutanena ba a bakin kome ba
kuma waɗanda suka mallake su sun yi musu ba’a,
Kullum ana cin gaba da yin wa sunana saɓo.
6 Saboda haka mutanena za su san sunana;
saboda haka a wannan rana za su san
cewa ni ne wanda ya faɗa wannan.
I, ni ne.”
7 Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu
a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi
waɗanda suke shelar salama,
waɗanda suke kawo labari mai daɗi,
waɗanda suke shelar ceto,
waɗanda suke ce wa Sihiyona,
“Allahnki yana mulki!”
8 Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu;
tare sun yi sowa ta farin ciki.
Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona,
za su gan shi da idanunsu.
9 Ku ɓarke cikin waƙoƙin farin ciki gaba ɗaya,
kangonki na Urushalima,
gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa,
ya fanshi Urushalima.
10 Ubangiji zai nuna hannunsa mai tsarki a fili
a idanun dukan al’ummai,
da kuma dukan iyakokin duniya za su gani
ceton Allahnmu.
11 Ku fita, ku fita daga can!
Kada ku taɓa wani abu marar tsarki!
Ku fita daga cikinta ku zama da tsarki,
ku da kuke ɗaukan kayan aikin Ubangiji.
12 Amma ba za ku fita a gaggauce ba
ko ku tafi da gudu;
gama Ubangiji zai ja gabanku,
Allah na Isra’ila zai kasance mai tsaron bayanku.
Wahala da kuma ɗaukakar bawan
13 Duba, bawana zai aikata abubuwa da hikima;
za a tā da shi a kuma ɗaga shi da ɗaukaka ƙwarai.
14 Kamar dai yadda aka kasance da mutane masu yawa waɗanda suka giggice sa’ad da suka gan shi,
kamanninsa ya lalace ƙwarai fiye da na kowane mutum
siffarsa kuma ta yi muni fiye da yadda ta mutum take,
15 haka zai ba al’ummai masu yawa mamaki,
sarakuna kuma za su riƙe bakunansu don mamaki.
Gama abin da ba a faɗa musu ba, shi za su gani,
kuma abin da ba su ji ba, shi za su fahimta.