57
1 Mai adalci yakan mutu,
ba kuwa wanda yakan yi tunani a zuciyarsa;
an kwashe mutanen kirki,
ba kuwa wanda ya fahimta
cewa an kwashe masu adalci
don a tsame su daga mugunta.
2 Waɗanda suke aikata abin da yake daidai
sukan shiga da salama;
sukan huta yayinda suka kwanta cikin kabari.
3 “Amma ku, ku matso nan, ku ’ya’ya maza na masu sihiri,
ku zuriyar mazinata da karuwai!
4 Wane ne kuke yi wa ba’a?
Ga wa kuke masa gwalo
kuna kuma fitar da harshe?
Ashe, ku ba tarin ’yan tawaye ba ne,
zuriyar maƙaryata?
5 Kuna cike da muguwar sha’awa mai ƙonawa a cikin itatuwan oak
da kuma a ƙarƙashin kowane itace mai inuwa;
kuna miƙa hadayar ’ya’yanku a rafuffuka
da kuma a ƙarƙashin tsagaggun duwatsu.
6 Gumakan da suke cikin duwatsu masu sulɓi su ne rabonku;
su ɗin, su ne rabonku.
I, gare su kuka kwarara hadayu na sha
kuka kuma miƙa hadayu na gari.
Saboda waɗannan abubuwa, zan yi haƙuri?
7 Kun yi gadonku a dogayen duwatsu masu tsayi da kuma a tudu mai tsawo;
a can kuka haura don ku miƙa hadayunku.
8 A bayan ƙofofi da madogaran ƙofofi
kuka kafa alamun gumakanku.
Kuka yashe ni, kuka kware gadonku,
kuka kwanta a kansa kuka fadada shi;
kuka kuma ƙulla yarjejjeniya da waɗanda kuke ƙaunar gadajensu,
kuka dubi tsiraicinsu.
9 Kuka tafi wurin Molek da man zaitun
kuka kuma riɓaɓɓanya turarenku.
Kuka aika jakadunku can da nisa;
kuka gangara zuwa cikin kabari kansa!
10 Kuka gaji cikin dukan al’amuranku,
amma ba ku iya cewa, ‘Aikin banza ne ba.’
Kuka sami sabuntar ƙarfinku,
ta haka ba ku suma ba.
11 “Wa ya sa ku fargaba, kuna jin tsoro
har kuka yi mini ƙarya,
ba ku kuma tuna da ni ba
balle ku yi tunanin wannan a zukatanku?
Ba don na daɗe ina shiru ba ne
ya sa ba kwa tsorona?
12 Zan bayyana adalcinku da kuma ayyukanku,
ba kuwa za su amfane ku ba.
13 Sa’ad da kuka nemi taimako,
bari tarin gumakanku su cece ku!
Iska za tă kwashe dukansu tă tafi,
ɗan numfashi kawai zai hura su.
Amma mutumin da ya mai da ni mafakarsa
zai gāji ƙasar
ya kuma mallaki dutsena mai tsarki.”
Ta’aziyya don mai tuba
14 Za a kuma ce,
“Ku gina, ku gina, ku gyara hanya!
Ku kawar da abubuwan sa tuntuɓe a hanyar mutanena.”
15 Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa
wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne,
“Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri,
amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu,
don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u
in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.
16 Ba zan tuhume su har abada ba,
ba kuwa kullum zai yi fushi ba,
gama a haka ruhun mutumin zan yi suma a gabana,
shi numfashin mutumin da na halitta.
17 Na yi fushi saboda kwaɗayin zunubinsa;
na yi masa horo, na kuma ɓoye fuskata saboda fushi,
duk da haka ya ci gaba da ayyukan zunubinsa.
18 Na ga al’amuransa, amma zan warkar da shi;
zan bi da shi in mayar da ta’aziyya a gare shi,
19 ina ƙirƙiro yabo a leɓunan masu makoki a Isra’ila.
Salama, salama, ga waɗanda suke nesa da kuma kusa,”
in ji Ubangiji. “Zan kuma warkar da su.”
20 Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku,
wanda ba ya natsuwa,
wanda raƙumansa sukan kawo gurɓacewa da tabo.
21 “Babu salama ga mugaye,” in ji Allahna.