58
Azumi na gaskiya
“Ku yi ihu da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa.
Ku tā da muryarku kamar busar ƙaho.
Ku furta wa mutanena tawayensu
da kuma ga gidan Yaƙub zunubansu.
Gama kowace rana suna nemana;
suna marmarin sanin hanyoyina,
sai ka ce al’ummar da take yin abin da yake daidai
ba ta kuma yashe umarnan Allahnta ba.
Sun nemi shawarwaran da suke daidai daga gare ni
suna kuma marmari Allah ya zo kusa da su.
Suna cewa, ‘Don me muka yi azumi,
ba ka kuma gani ba?
Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu,
ba ka kuma lura da wannan ba?’
 
“Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama
kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata.
Azuminku yakan ƙare a faɗa da kuma hargitsi,
kuna ta naushin juna da mugayen naushe-naushe.
Ba za ku iya azumi kamar yadda kuke yi a yau
ku zaci za a ji muryarku can sama.
Irin azumin da na zaɓa ke nan,
rana guda kawai don mutum ya ƙasƙantar da kansa?
Sunkuyar da kanku kamar iwa kawai
kuna kuma kwance a tsummoki da toka?
Abin da kuke kira azumi ke nan
rana yardajje ga Ubangiji?
 
“Irin azumin da na zaɓa shi ne,
a kunce sarƙoƙin rashin adalci
a kuma kunce igiyoyin karkiya,
a ’yantar da waɗanda ake zalunta
a kuma kakkarye kowace karkiya?
Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata
ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli,
sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura,
kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya?
Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir,
warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan;
sa’an nan adalcinku* zai tafi a gabanku,
ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya.
Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa;
za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan.
 
“In kuka kawar da karkiyar zalunci,
kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu,
10 in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata
kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani,
sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu
darenku kuma zai zama kamar tsakar rana.
11  Ubangiji zai bishe ku kullum;
zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana
ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku.
Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa,
kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa.
12 Mutanenku za su sāke gina kufai na da
su kuma daga tsofaffin harsashai;
za a ce da ku Masu Gyaran Katangar da ta Rushe,
Masu Farfaɗo da Tituna da kuma Wuraren zama.
 
13 “In kun kiyaye ƙafafunku daga take Asabbaci
da kuma daga aikata abin da kuka gan dama a ranata mai tsarki,
in kuka kira Asabbaci ranar murna
rana mai tsarki ta Ubangiji kuma mai bangirma,
in kuka girmama ta ta wurin ƙin yin abin da kuka gan dama
da kuma yin al’amuranku ko yin mugayen maganganu,
14 sa’an nan za ku yi farin ciki a cikin Ubangiji,
zan kuma sa ku a kan maɗaukaka ƙasashe
ku kuma yi biki a gādon mahaifinku Yaƙub.”
Ni Ubangiji ne na faɗa.
* 58:8 Ko kuwa Mai Adalcinka