62
Sabon sunan Sihiyona
Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba,
saboda Urushalima ba zan huta ba,
sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya,
cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske.
Al’ummai za su ga adalcinki,
sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki;
za a kira ki da sabon suna
sunan da bakin Ubangiji zai ambata.
Za ki zama rawanin daraja a hannun Ubangiji,
rawanin sarauta a hannun Allahnki.
Ba za a ƙara ce da ke Yasasshiya ba,
ko a kira ƙasarki Kango.
Amma za a ce da ke Hefziba*
ƙasarki kuma Bewula;
gama Ubangiji zai ji daɗinki,
ƙasarki kuma za tă yi aure.
Kamar yadda saurayi kan auri yarinya,
haka ’ya’yanki maza za su aure ki;
kamar kuma yadda ango yakan yi farin ciki da amaryarsa,
haka Allahnki zai yi farin ciki da ke.
Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima;
ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana.
Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji,
kada ku ba kanku hutu,
kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima
ya kuma mai da ita yabon duniya.
 
Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama
ta hannunsa kuma mai iko cewa,
“Ba zan ƙara ba da hatsinki
ya zama abinci ga abokan gābanki ba,
baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin
wanda kika sha wahala samu ba;
amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi
su kuma yabi Ubangiji,
waɗanda kuma suka tattara ’ya’yan inabi za su sha shi
a filayen wurina mai tsarki.”
 
10 Ku wuce, ku wuce ƙofofi!
Ku shirya hanya saboda mutane.
Ku gina, ku gina babbar hanya!
Ku kawar da duwatsu.
Ku ɗaga tuta saboda al’ummai.
 
11 Ubangiji ya yi shela
ga iyakokin duniya cewa,
“Faɗa wa Diyar Sihiyona,
‘Ga Mai Cetonki yana zuwa!
Ga ladarsa tana tare da shi,
sakamakonsa yana raka shi.’ ”
12 Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane,
Fansassu na Ubangiji;
za a kuma ce da ke Wadda Aka Nema
Birnin da Ba Za a Ƙara Yashe ta ba.
* 62:4 Hefziba yana nufin farin cikina yana a cikinta. 62:4 Bewula yana nufin wadda ta yi aure. 62:5 Ko kuwa Mai gini