63
Ranar ɗaukan fansa da kuma ceto na Allah
1 Wane ne wannan mai zuwa daga Edom,
daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa?
Wane ne wannan, sanye cikin daraja,
tafe cikin girmar ƙarfinsa?
“Ni ne, mai magana cikin adalci,
mai ikon ceto.”
2 Me ya sa rigunanka suka yi ja,
sai ka ce na wanda yake tattaka ’ya’yan inabi?
3 “Na tattake ’ya’yan inabi ni kaɗai;
cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni.
Na tattake su cikin fushina
Na matse su cikin hasalata;
jininsu ya fantsamar wa rigunana,
na kuma ɓata dukan tufafina.
4 Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata,
kuma shekarar fansata ta zo.
5 Na duba, amma babu wanda zai taimaka,
na yi mamaki cewa ba wanda ya goyi baya;
saboda haka hannuna ya yi mini ceto,
fushina kuma ya rayar da ni.
6 Na tattake al’ummai cikin fushina;
cikin hasalata kuma na sa sun bugu
na kuma zub da jininsu a ƙasa.”
Yabo da addu’a
7 Zan ba da labarin alherin Ubangiji,
ayyukan da suka sa a yabe shi,
bisa ga dukan abubuwan da Ubangiji ya yi mana,
I, ayyuka masu kyan da ya yi
domin gidan Isra’ila,
bisa ga jinƙansa da yawan alheransa.
8 Ya ce, “Babu shakka su mutanena ne,
’ya’ya maza waɗanda ba za su ruɗe ni ba”;
ta haka ya zama Mai Cetonsu.
9 Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu,
mala’ikan da yake gabansa ya cece su.
Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su;
ya kuma ɗaga su ya riƙe su
dukan kwanakin dā
10 Duk da haka suka yi tawaye
suka ɓata wa Ruhu Mai Tsarki rai.
Saboda haka ya juya ya kuma zama abokin gābansu
shi kansa kuma ya yaƙe su.
11 Sa’an nan mutanensa suka tuna kwanakin dā,
kwanakin Musa da mutanensa,
ina yake shi wanda ya fitar da su ta teku,
da makiyayan garkensa?
Ina shi yake wanda ya sa
Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu,
12 wanda ya aika hannu ɗaukakarsa mai iko
ya kasance a hannun dama na Musa,
wanda ya raba ruwaye a gabansu,
don yă sami wa kansa madawwamin suna,
13 wanda ya bishe su cikin zurfafa?
Kamar doki a fili,
ba su yi tuntuɓe ba;
14 kamar shanun da suke gangarawa zuwa kwari,
haka Ruhun Ubangiji ya ba su hutu.
Ga yadda ka bishe mutanenka
don ka ba wa kanka suna mai ɗaukaka.
15 Ka duba daga sama ka gani
daga kursiyinka da yake bisa, mai tsarki da kuma mai ɗaukaka.
Ina kishinka da kuma ikonka?
Ka janye juyayi da kuma tausayin da kake yi mana daga gare mu.
16 Amma kai Ubanmu ne,
ko Ibrahim bai san mu ba
Isra’ila kuma bai yarda da mu ba;
kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu,
Mai Fansarmu tun fil azal ne sunanka.
17 Don me, ya Ubangiji, ka sa muna barin hanyoyinka
muka kuma taurare zukatanmu don kada mu girmama ka?
Ka komo domin darajar bayinka,
kabilan da suke abin gādonka.
18 Gama a ɗan lokaci mutanenka suka mallaki wurinka mai tsarki,
amma yanzu abokan gābanmu sun tattake wurinka mai tsarki.
19 Mu naka tun fil azal;
ba ka taɓa yin mulki a kansu ba,
ba a taɓa kira su da sunanka ba.