21
Ayuba
Sai Ayuba ya amsa,
“Ku saurare ni da kyau;
bari wannan yă zama ta’aziyyar da za ku ba ni.
Ku ba ni zarafi in yi magana,
bayan na gama sai ku yi ba’arku.
 
“A wurin mutum ne na kawo kukana?
Don me ba zan kāsa haƙuri ba?
Ku dube ni, ku kuma yi mamaki;
ku rufe bakina da hannunku.
Lokacin da na yi tunanin wannan,
sai in ji tsoro; jikina yă fara rawa.
Don me mugaye suke rayuwa har su tsufa,
suna kuma ƙaruwa da iko?
Suna ganin ’ya’yansu suna girma,
suna ganin jikokinsu suna tasowa a kan idanunsu.
Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba.
Kuma Allah ba ya ba su horo.
10 Shanunsu ba sa fasa haihuwa;
suna haihuwa ba sa yin ɓari.
11 Suna aika ’ya’yansu kamar garke;
’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle.
12 Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya;
suna jin daɗin busar sarewa.
13 Suna yin rayuwarsu cikin arziki
kuma su mutu cikin salama.
14 Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’
Ba ma so mu san hanyoyinka.
15 Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa?
Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?
16 Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba
saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.
 
17 “Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa?
Sau nawa bala’i yake auka masa,
ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?
18 Sau nawa suke zama kamar tattaka a iska,
ko kuma kamar ƙura da iskar hadari take kwashewa?
19 An ce ‘Allah yana tara wa ’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’
Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka!
20 Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka;
bari yă sha daga fushin Maɗaukaki.
21 Ko zai damu da iyalin da ya bari a baya
sa’ad da kwanakinsa suka ƙare?
 
22 “Wani zai iya koya wa Allah ilimi
tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?
23 Wani mutum zai mutu cikin jin daɗi
da kwanciyar hankali,
24 jikinsa ɓulɓul,
ƙasusuwansa da alamar ƙarfi.
25 Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai,
bai taɓa jin daɗin wani abu mai kyau ba.
26 Dukansu kuwa za a bizne su a ƙasa,
kuma tsutsotsi za su cinye su.
 
27 “Na san duk abin da kuke tunani,
yadda za ku saɓa mini.
28 Kuna cewa, ‘Yanzu ina gidan babban mutumin nan,
tenti wurin da mugaye suke zama?’
29 Ba ku taɓa tambayar waɗanda suke tafiya ba?
Ba ku kula da labaransu,
30 cewa an kāre mugu daga ranar bala’i,
an kāre shi daga ranar fushi?
31 Wane ne yake gaya masa abin da ya yi?
Wane ne yake rama abin da ya yi?
32 Za a bizne shi a kabari,
a kuma yi tsaron kabarinsa.
33 Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali;
dukan jama’a suna binsa,
da yawa kuma suna gabansa.
 
34 “Saboda haka ta yaya za ku iya yi mini ta’aziyya
da surutan banzan nan naku? Babu wani abu cikin amsarku sai ƙarya!”