22
Elifaz
Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,
“Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah?
Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi?
Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne?
Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce?
 
“Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka
ya kuma bari haka yă same ka?
Ba muguntarka ce ta yi yawa ba?
Ba zunubanka ne ba iyaka ba?
Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili;
ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara.
Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba
kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci.
Ko da yake kai mai ƙarfi ne, ka mallaki ƙasa,
mutum mai martaba kuma, kana zama cikin ƙasarka.
Ka kori gwauraye hannu wofi,
ka kuma karya ƙarfin marayu.
10 Shi ya sa kake kewaye da tarkuna,
shi ya sa ka cika da tsoron mugun abin da zai auko maka.
11 An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani,
shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka.
 
12 “Ba Allah ne a can sama ba?
Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama!
13 Duk da haka ka ce, ‘Me Allah ya sani?
A cikin duhu ne yake shari’a?
14 Gajimare ya rufe shi, saboda haka ba ya ganinmu
lokacin da yake takawa a cikin sammai.’
15 Za ka ci gaba da bin tsohuwar hanyar
da mugayen mutane suka bi?
16 An ɗauke su kafin lokacinsu yă cika,
ruwa ya share tushensu.
17 Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu!
Me Maɗaukaki zai yi mana?’
18 Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau,
saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.
 
19 “Masu adalci suna gani ana hallaka mugaye, suna jin daɗi;
marasa laifi suna yi musu ba’a, suna cewa,
20 ‘Ba shakka an hallaka maƙiyanmu,
wuta kuma ta ƙona dukiyarsu.’
 
21 “Ka miƙa kanka ga Allah ka samu salamarsa;
ta haka ne arziki zai zo maka.
22 Ka bi umarnin da zai fito daga bakinsa
kuma ka riƙe maganarsa a cikin zuciyarka.
23 In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke.
In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.
24 Ka jefar da zinariyarka a ƙasa,
ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,
25 sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka,
zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.
26 Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki
daga wurin Maɗaukaki,
ku kuma ɗaga idanunku ga Allah
27 Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka,
kuma za ka cika alkawuranka.
28 Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki,
haske kuma zai haskaka hanyarka.
29 Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’
Sa’an nan zai ceci masu tawali’u.
30 Zai ceci wanda ma yake mai laifi,
wanda zai tsirar da shi ta wurin tsabtar hannuwanka.”